Najeriya da ECOWAS sun yi tir da hambarar da Gwamnati da Soji su ka yi a Mali

Najeriya da ECOWAS sun yi tir da hambarar da Gwamnati da Soji su ka yi a Mali

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi tir da abin da ya faru a kasar Mali inda sojoji su ka tsare shugaban kasa, Ibrahim Keita da Firayim Minista, Boubou Cisse.

A dalilin wannan juyin mulki da sojoji su ka yi, shugaban kasar Mali ya yi murabus. Hakan na zuwa ne bayan tsawon lokaci ana fama da matsaloli a kasar yammacin Afrikar.

Ministan harkokin wajen Najeriya, Geoffrey Onyeama ya nuna rashin jin dadin hambarar da gwamnati mai-ci ta yi, ya ce dole kundin tsarin mulki ya yi aiki a Mali.

Geoffrey Onyeama ya bayyana wannan a ranar Laraba a shafinsa na Twitter a madadin gwamnati.

Ya ce: “Gwamnatin tarayya ta yi Allah-wadai ta kowane fuska da juyin mulkin da ya faru a Makon jiya, kuma ta na kira da ayi maza a koma amfani da kundin tsarin mulki.”

“Mu na maraba da tada dakarun Sojojin ECOWAS da aka yi.” Inji ministan na Najeriya.

Shugaban majalisar dinkin Duniya, Antonio Guterres ya yi irin wannan kira na cewa ayi maza a fito da shugaban kasa Keita da firyamin ministan Mali, Cisse.

KU KARANTA: Wanene Shugaban Mali da aka yi wa juyin mulki?

Najeriya da ECOWAS sun yi tir da hambarar da Gwamnati da Soji su ka yi a Mali
Shugaba Ibrahim Boubacar Kéita ya ajiye mulki
Asali: UGC

Gwamnatin Amurka da Faransa ta bakin shugaba Emmanuel Macron da Jakada Peter Pham, sun soki lamarin, sun koka da yadda aka yi amfani da sojoji wajen keta doka.

Kungiyar ECOWAS ta ce ba za ta amince da juyin mulkin ba, don haka ta yi kira ga sojoji su koma gidan baraki, sannan su saki shugaba Ibrahim Boubacar Kéita da iyalinsa.

A ranar Laraba ne ECOWAS ta sanar cewa ta dauki matakin dakatar da kasar Mali daga duk wata shawara da za a dauka a yankin, har sai lokacin da farar hula ta koma kan mulki.

Bayan haka, kungiyar kasashen yammacin Afrikar ta rufe duk iyakokin kasa da na saman kasar, sannan ta yanke kowace irin alaka da huldar kasuwanci tsakaninta da Mali.

Hukumar dillacin labarai na Najeriya ta rahoto ECOWAS ta bakin darektanta na sadarwa ta na kira a hukunta sojojin da su ka kifar da gwamnati mai-ci a Mali.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel