Yanzu Yanzu: Dakarun sojoji sun kashe shugabannin ISWAP a Borno

Yanzu Yanzu: Dakarun sojoji sun kashe shugabannin ISWAP a Borno

- Dakarun rundunar sojin Najeriya sun dagargaji ‘yan ta’addan ISWAP a jihar Borno

- Rundunar Operation Hail Storm ne suka aiwatar da aikin inda suka kashe ‘yan ta’adda 20

- Sun kuma tarwatsa cibiyar dabaru na ISWAP a Bukar Meram

Rundunar sojojin Najeriya ta ce an kashe mambobin kungiyar ‘yan ta’adda na ISWAP su 20 a wani harin sama.

John Enenche, jagoran sashin labarai na ayyukan rundunar, ya bayyana hakan a cikin wani jawabi a ranar Laraba.

Ya ce harin wanda ya wakana a ranar Litinin ya gudana ne a karkashin Operation Hail Storm, rundunar Operation Lafiya Dole na sama.

Enenche ya kara da cewar jirgin rundunar sojin sama sun lalata Bukar Meram, wani cibiyar dabaru na shugabannin ISWAP.

Ya ci gaba da cewa akalla ‘yan ta’adda 20 harda shugabanninsu aka kakkabe a harin.

KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun kashe sojoji 3 da 'dan sa kai 1 a Niger

Yanzu Yanzu: Dakarun sojoji sun kashe shugabannin ISWAP a Borno
Yanzu Yanzu: Dakarun sojoji sun kashe shugabannin ISWAP a Borno
Asali: UGC

A ci gaba da kai hare-hare ta sama wanda Operation Hail Storm, rundunar Operation Lafiya Dole na sama suke kaiwa, sun yi nasarar kashe wasu kwamandojin ‘yan ta’addan ISWAP sannan suka lalata cibiyarsu a Bukar Meram a iyakar tafkin Chadi da ke jihar Borno. An kuma kashe wasu da dama a Dole, wani yanki a kudancin jihar Borno,” in ji shi.

An aiwatar da ayyukan ne a ranar 17 ga watan Agusta 2020 sakamakon bayanai abun dogaro da suka samu da ke nuna dawowar ayyukan ta’addanci a yankunan biyu.

“Rundunar sojin sama ta kai hari Bukar Meram, wani babban cibiyar dabarun ISWAP da kuma mazaunan mayakan kungiyar da dama da wasu shugabanninsu, sannan ta bude wuta ta sama wanda hakan ya yi sanadiyar lalata ginin da kuma kashe ‘yan ta’adda da dama tare da shugabanninsu.

“An gudanar da harin Dole ne bayan binciken ISR ya nuna ayyuka na gudana a yankin bayan sauya wurin wasu ‘yan ta’adda daga wuraren da ke kusa na Kokiwa da Yale.

“Jirgin ISR ya gano akalla ‘yan ta’adda 20 a yankin, sakamakon harin rundunar NAF.”

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel