Ibrahim Keita: Shugaban da ya yi murabus bayan Sojojin Mali sun yi juyin-mulki

Ibrahim Keita: Shugaban da ya yi murabus bayan Sojojin Mali sun yi juyin-mulki

Shugaban kasar Mali, Ibrahim Boubacar Keita ya bada sanarwar murabus a ranar 18 ga watan Agusta. Keita ya ajiye mulki ne saboda gujewa zubar da jini a kasarsa.

Wanene Ibrahim Keita wanda yanzu ya sauka daga kan mulki?

1. Haihuwa

An haifi Ibrahim Boubacar Keïta ne a ranar 29 ga watan Junairu, 1945. A lokacin da aka kifar da gwamnatinsa da karfin tsiya, ya na da shekaru 75.

Mahaifinsa ma’aikacin gwamnati ne, ya kuma tashi a garin Koutiala da ke kudancin Mali. Kakansa tsohon soja ne wanda ya je yakin Duniya na farko.

2. Karatu

Ibrahim Keita wanda aka fi sani da IBK ya karanta ilmin adabi a gida watau Mali da kuma kasashen waje kamar Sanagal, ya kuma yi karatu har a Faransa.

3. Aiki

Bayan ya kammala makaranta, Ibrahim Keita ya samu aiki da kungiyar EU ta kasashen Turai. Keita ya yi aiki da kungiyar a matsayin mai bada shawara.

4. Siyasa

Keita ya na cikin wadanda su ka yi wa tsohon shugaban Mali, Moussa Traore adawa. Ya zama Firayim Ministan Mali tsakanin 1994 zuwa shekarar 2000 inda ya yi murabus.

KU KARANTA: UN za ta yi zama na musamman bayan kifar da Gwamnatin Mali

Ibrahim Keita: Shugaban da ya yi murabus bayan Sojojin Mali sun yi juyin-mulki
Ibrahim B. Keita Hoto: UN
Asali: UGC

5. Majalisa

A 2002, Keita ya lashe kujerar majalisar tarayya mai wakiltar yankin Bamako. Wannan ya sa ya zama shugaban majalisar Mali, kuma shugaban kungiyar ‘yan Majalisar Afrika.

6. Shugaban kasa

Bayan ya samu farin jini a lokacin Alpha O. Konare, Keita ya yi nasarar cin zaben shugaban kasar Mali a 2013 da 2018. Kafin nan ya yi takara amma ya sha kashi a 2002 da 2007.

Keita ya nada Oumar Tatam a matsayin Firayim Minista a 2013. Bayan ritayar Tatam, ya tafi da Moussa Mara, Modibo Keita, Soumeylou Boubéye da kuma Dr Boubou Cissé.

7. Juyin-mulki

A makon nan ne sojojin tawaye su ka kifar da gwamnatin Mali bayan an dade ana ta rikici a kasar.

Keïta ya na auren uwargidar Mali, Keïta Aminata Maiga, kuma sun haifi ‘ya ‘ya hudu. Daga ciki har da wanda ya taba rike kujerar 'dan majalisar tarayya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel