Ronald Koeman zai zama sabon Kocin Barcelona, Quique Setien zai yi waje

Ronald Koeman zai zama sabon Kocin Barcelona, Quique Setien zai yi waje

- Rahotanni sun ce ana shirin sallamar Quique Setien daga kungiyar Barcelona

- Bisa dukkan alamu kan kulob din ya hadu a kan Ronald Koeman a matsayin koci

- Koeman, Mauricio Pochettino, ko Xavi ake tunanin za su karbi aikin horaswar

Rahotanni daga jaridun kasashen Turai sun nuna kungiyar Barcelona za ta nada kocin kasar Holland, Ronald Koeman a matsayin sabon kocinta a cikin farkon makon nan.

Shararren ‘dan jaridar nan Fabrizio Romano ya ce Barcelona ta na shirin sallamar Quique Setien daga kujerar mai horas da manyan ‘yan kwasan kwallon kafanta.

Hakan na zuwa ne bayan Bayern Munich ta kunyata Barcelona a gasar cin kofin Nahiyar Turai. Bayern ta lallasa kungiyar Sifen din ne da ci 8-2 kwanan nan.

Tsohon kocin Everton, Ronald Koeman ya kwantawa Barcelona a rai, kuma rahotanni sun ce za a tsaida shi a matsayin sabon koci da zarar an yi waje da Quique Setien.

Wani kocin da ake hangen zai iya rike Barcelona a wannan lokaci shi ne Mauricio Pochettino wanda kungiyar Tottenham ta sallama a karshen shekarar da ta wuce.

KU KARANTA: Bayern ta ci mutuncin Barcelona, ta yi mata cin Allah ya - isa

Ronald Koeman zai zama sabon Kocin Barcelona, Quique Setien zai yi waje
A karon farko tun 2007, Barcelona za ta tashi babu kofi
Asali: Getty Images

Matsalar da Barcelona za ta samu wajen daukar hayan Mauricio Pochettino shi ne da wuya ya yarda ya yi aiki da kungiyar a matsayinsa na tsohon kocin Espanyol.

Tsohon ‘dan wasa Xavi Hernandez wanda ya yi ritaya daga kungiyar 2014 ya na tare da Al-Sadd, kuma bai da niyyar barin kasar Qatar a daidai wannan lokaci.

Hakan ya sa ake ganin Ronald Koeman ya zama sabon kocin Barcelona ya gama. Kocin mai shekaru 57 ya bugawa kungiyar kwallo tsakanin shekarar 1989 zuwa 1998.

Koeman ya kuma yi aiki da Barcelona a matsayin mataimakin koci daga 1998 zuwa 2000. Bayan nan ya rike kungiyoyi irinsu Ajax, Benfica, PSV, Valencia, AZ, da Feynoord.

Haka zalika tsakanin 2014 zuwa 2017, Ronald Koeman ya yi aiki a Ingila, ya horas da kungiyoyin Southampton da Everton a gasar Firimiya, daga nan kasarsa ta yi hayarsa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel