Bidiyo: Sojoji sun yi luguden wuta a sansanin 'yan ta'addan Ansaru a dajin Kuduru

Bidiyo: Sojoji sun yi luguden wuta a sansanin 'yan ta'addan Ansaru a dajin Kuduru

Dakarun Sojojin Saman Najeriya na musamman ta Operation Thunder Strike ta kashe yan ta'adda da dama a sansaninsu da ke dajin Kuduru na jihar Kaduna a cewar Hedkwatan Tsaro, DHQ.

Mai magana da yawun rundunar tsaron, John Enenche ne ya bayyana hakan cikin sanarwar da ya fitar a ranar Asabar 15 ga watan Agusta a Abuja.

Mr Enenche ya ce, an kai hare haren saman ne a ranar 13 ga watan Agusta bayan samun sahihan bayannan sirri da ke nuna yan taaddan na kungiyar Ansaru da ke da alaka da yan bindiga karkashin jagorancin Mallam Abba ke taruwa.

Ya ce naurar leken asiri ta sama da aka yi amfani da ita a yankin ya nuna 'yan ta'addan da dama a wurin, wasu daga cikinsu na rike na makamai a cikin dajin.

Bidiyo: Sojoji sun yi luguden wuta a sansanin yan ta'addan Ansar a dajin Kaduna
Bidiyo: Sojoji sun yi luguden wuta a sansanin yan ta'addan Ansar a dajin Kaduna. Hoto daga Daily Nigerian
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Kotun zaɓe ta yi watsi da ƙarar ɗan takarar AD, ta tabbatar da nasarar Diri

A cewarsa, Rundunar Sojojin Sama, NAF, sun yi amfani da jiragensu masu saukan ungulu da jiragen yaki suka yi wa sansanin luguden wuta.

"An kashe yan ta'addan da dama a yayin da jiragen saman ke yin luguden wuta a sansanin, wasu da aka gano suna kokarin tsere wa suma an bi su an karasa su," in ji shi.

Ga bidiyon harin a kasa;

A wani rahoton, kun ji cewa Sarkin Gusau a jihar Zamfara, Dakta Ibrahim Bello ya nada babban hafsan sojojin ƙasa na Najeriya, Laftanat Janar Yusuf Tukur Buratai sarautar gargajiya ta Ƙauran Gusau.

Sarkin ya ce an naɗa Buratai wannan sarautar ne saboda jajircewarsa wurin kawo karshen hare-haren ƴan bindiga da ma ta'addanci a yankin arewacin Najeriya.

A jawabin da ya yi yayin rufe bukukuwar ranar sojojin Najeriya ta shekarar 2020 da aka fara a ranar 4 ga watan Yulin wannan shekarar, Sarkin na Gasau ya ce jajircewar sojojin ya saka mutane da dama a arewa suna iya barci da idanun su biyu a rufe.

A cewarsa, a baya, mutanen yankin su ba su iya barci cikin dare saboda tsoron harin ƴan bindiga da sauran ɓata gari.

"Na gamsu kuma ina murna da farin ciki bisa tanade-tanade da tsarin da na gani a ƙasa a yanzu," in ji shi.

Sarkin ya tuna cewa akwai lokacin da mutane ba su iya barci kuma manoma ba su zuwa gonakin su amma a halin yanzu suna iya yin hakan saboda sojoji da aka kawo jihar da kuma kafa atisayen Sahel Sanity a yankin Arewa maso Yamma.

"Allah zai tsare kuma ya kare sojojin mu domin su kare al'umma, Allah kadai zai iya basu nasara duba da shiri da kwarewar da suke nuna wa."

Sarkin ya bayyana cewa ya yi imanin sojojin za su yi nasara a kan ƴan bindigan da sauran ɓata gari a yankin sakamakon atisayen da suka ƙaddamar don kawar da laifuka a yankin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164