Nadin Bashir Magashi na Isa Garba a Makarantar NDA ya bar baya da kura

Nadin Bashir Magashi na Isa Garba a Makarantar NDA ya bar baya da kura

An samu hargitsi a dalilin nadin da ministan tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi mai ritaya ya yi na sabon shugaban boko na makarantar sojojin Najeriya ta NDA.

Jaridar Leadership ta yi wani bincike inda ta gano cewa ministan tsaro na kasa, Bashir Magashi, ya sabawa ka’ida da dokar aiki wajen nada shugaban NDA da ke Kaduna.

Janar Bashir Magashi ya matsa a kan cewa sai an nada Farfesa Isa Garba na tsangayar fasaha a jami’ar Bayero ta Kano a matsayin sabon shugaban makarantar sojojin kasa.

Abin mamakin shi ne Isa Garba bai shiga cikin sahun Farfesoshi biyar wadanda aka tantance kwanakin baya da nufin fito da sabon shugaban makarantar NDA ba.

Wadanda aka tantance, aka kuma yi wa jarrabawa su ne: David Oluwatoba Alabi, Sunday Olawole Okeniyi, Sydney Chinedu Osuala, Jonathan Maduka Nwaedozie da Adam Okene Ahmed.

Dukkaninsu manyan malamai ne da ke aiki a sashen siyasa, kimiyya, lissafi, ilmin gafaka da tarihi a wannan makaranta kamar yadda jaridar Leadership ta bayyana a jiya.

Daga baya an cire Farfesa Nwaedozie saboda shekarun ritayarsa za su cika kafin ya iya gama wa’adinsa. Bayan haka an gudanar da jarrabawa wanda Okene Ahmed ya zo na farko.

KU KARANTA: Sowore zai jawowa kansa shiga kotu da Shugaban 'Yan Sanda

Nadin Bashir Magashi na Isa Garba a Makarantar NDA ya bar baya da kura
An saba doka wajen nadin Shugaban NDA
Asali: Twitter

A sakamakon haka aka nada Adam Okene Ahmed ya zama mukaddashin shugaban boko na makarantar. Abin da kurum ya rage shi ne majalisar makarantar ta tabbatar da nadin.

Kwatsam sai aka ji cewa ministan tsaro wanda shi ne shugaban majalisar da ke lura da NDA, ya yi fatali da Adam Okene Ahmed, ya nada Farfesa Isa Garba a matsayin shugaba.

Ana zargin cewa akwai hannun fadar shugaban kasa a wannan nadi da aka yi wanda ya sabawa ka’ida. Jaridar ta ce babu hujja mai karfi da zai iya tabbatar da wannan zargi.

Wata majiyar ta ce ministan ya yi amfani da karfin ikonsa ne ya nada mutumin Kano ya rike makarantar sojojin kasar. A wani kaulin, ana zargin cewa Garba ‘da ne a wurin Magashi.

Da aka tuntubi mai magana da yawun bakin makarantar, Manjo Abubakar Abdullahi, ya ce majalisar da ministan tsaro ya ke zaune kanta ne ta ke da ta cewa game da nadin.

Sakataren din-din-din na ma’aikatar tsaro, Sabiu Zakari, ya ce an bi doka wajen ba Isa Garba wannan mukami. A cewarsa kafin ya shiga ofis, Garba ya na cikin wadanda aka tantance.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel