Buhari, Oshiomhole, Boko Haram sun shiga jerin batutuwan da za a dade ana maganarsu

Buhari, Oshiomhole, Boko Haram sun shiga jerin batutuwan da za a dade ana maganarsu

Wannan shekara ta 2020 ta zo da abubuwan ban mamaki a Najeriya kamar yadda wani Bawan Allah ya rubuta a kafar sada bayanai na zamani.

Legit.ng Hausa ta dauko abubuwan ban al’ajabin da su ka faru inda aka ji kura ta na kiran kare maye tsakanin wata tsohuwar jami’ar gwamnati da ‘yan damfara.

A shekarar bana ne kuma reshe ya juye da mujiya a hukumar EFCC inda yanzu Ibrahim Magu ya ke kukan ana ci masa zarafi, abin da aka zarge shi da yi a baya.

A bangaren siyasa ma an ga abubuwan da su ka ba mutanen Najeriya mamaki a shekarar nan, daga zaben Edo zuwa gwamnatin APC mai mulki ta Muhammadu Buhari.

An kuma ji shugaban kungiyar ‘yan ta’addan Boko Haram ya na magana kamar yadda ya saba:

Duniya mai yayi:

1. Abubakar Shekau ya soki hukuncin shari’a

A watan Agusta kotun shari’a a Kano ta yankewa wani Yahaya Sharif-Aminu hukuncin kisa bayan an same shi da laifin batanci ga Musulunci. An ji Abubakar Shekau ya fito ya na sukar wannan hukunci duk da cewa kungiyarsa ta na ikirarin kira ga shari’a.

2. Sanata Godwill Akpabio ya zargi ‘Yan Majalisa da sata

Ministan Neja-Delta, Godwill Akpabio ya fito ya na zargin tsofaffin abokan aikinsa a majalisar kasar da laifin rashin gaskiya, ministan ya ce ana rabawa ‘yan majalisa kwangilolin NDDC.

3. Diezani Alison-Madukwe da ‘Yan Yahoo-Yahoo

Kwanakin baya aka ji Diezani Alison-Madukwe ta na kaca-kaca da matasa da su ke daukar masu zamba cikin aminci da damfara wasu abin koyi, sai dai ita kanta, ta na da zargin kashi a kanta.

KU KARANTA: Wayyo: Tsohon Shugaban EFCC Magu ya cigaba da kukan 'rashin adalci'

Buhari, Oshiomhole, Boko Haram sun shiga jerin batutuwan da za a dade ana maganarsu
An koma binciken tsohon Shugaban EFCC
Asali: UGC

4. APC, Ize-Iyamu da Godwin Obaseki

Adams Oshiomhole ya yi baram-baram da mutuminsa Godwin Obaseki wanda yanzu ya koma PDP, ya na kuma marawa Osagie Ize-Iyamu baya wanda ya yi wa kaca-kaca a lokacin ya na PDP.

5. Gwamnatin Buhai da kasar Mali

Shugaba Muhammadu Buhari ya sha alwashin shawo kan rikicin siyasar kasar Mali. A daidai wannan lokaci kasarsa ta na fama da matsanancin rashin tsaro musamman a yankin Arewa.

6. Binciken Ibrahim Magu

A cikin Yuli aka tunbuke Ibrahim Magu daga kujerar hukumar EFCC, kuma aka shiga bincikensa. Magu ya na kukan kwamitin binciken ba ya yi masa adalci, abin da aka zarge shi da yi a baya.

7. Tubabbun Boko Haram sun zama sha-lele

Gwamnatin Najeriya ta dauki wasu tubabbun ‘yan ta’addan Boko Haram ta koya masu sana’a domin su samu abin dogara. Wannan mataki ya bada mamaki, kuma bai samu karbuwa ba sosai.

8. Zulum: Sojoji da Boko Haram

Babagana Zulum na Borno ya zargi sojoji da kai masa hari a Baga. Ya ke cewa: “Ba zan kare hira ba sai na fadi abin da ya faru…. A iya sanina, babu Boko Haram, sojoji ne su ka rika harbe-harbe…”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel