Kungiyar Barcelona ta ce COVID-19 ta harbi wani daga cikin ‘Yan kwallonta

Kungiyar Barcelona ta ce COVID-19 ta harbi wani daga cikin ‘Yan kwallonta

An tabbatar da cewa wani ‘dan wasan kungiyar FC Barcelona ya kamu da cutar COVID-19 mai jawo wahalar numfashi.

Wannan labari ya zo wa kungiyar kwallon kafar da magoya bayanta ne a lokacin da ta ke shirin haduwa da Bayern Munich a Ranar Juma’a.

Rahotanni sun nuna cewa Barcelona ta bada wannan sanarwa ne a shafinta na yanar gizo a jiya ranar Laraba, 11 ga watan Agustan, 2020.

Barcelona ta ce wannan ‘dan wasa bai samu wata alaka da tawagar ‘yan kwallonta da za su tafi birnin Lisbon domin wasan kofin Turai ba.

“Bayan gwajin PCR da aka yi wa rukunin ‘yan wasanmu tara da za su fara wasan sharer fage na kaka mai zuwa a yau (ranar Talata a lokacin), sakamako ya nuna wani guda daga cikinsu ya na dauke da kwayar cutar COVID-19.”

Barcelona ta fitar da wannan jawabi ne a jiya da rana, ta na mai sanar da cewa ‘dan wasan na ta ya na nan garau ba tare da ya kwanta jinya ba.

KU KARANTA: Messi ya bugu a wasan Barcelona da Napoli

Har yanzu kungiyar ba ta bayyana sunan wannan ‘dan wasa da ya kamu da cutar COVID-19 ba.

“’Dan wasan bai sadu da wani daga cikin manyan ‘yan wasanmu da aka shirya za su tafi birnin Lisbon a ranar Alhamis domin wasan Turai ba.”

Bisa dukkan alamu karamin ‘dan wasa ne ya kamu da wannan cuta, ganin yadda kungiyar ta nuna ba ya cikin masu shiryawa wasan Bayern Munich.

Jawabin da kungiyar ta fitar ya shaidawa Duniya cewa an killace wannan ‘dan wasa a gidansa. Wannan zai taimaka wajen dakile yaduwar cutar.

Wani abin murna kuma shi ne ‘dan wasan gaban Barcelona, Ousmane Dembélé zai dawo bakin aiki bayan ya shafe watanni tara ya na jinya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel