Zanga-zangar yi wa Annabi batanci: An kashe mutum 3 a kasar Indiya

Zanga-zangar yi wa Annabi batanci: An kashe mutum 3 a kasar Indiya

Rahotanni da muke samu sun nuna cewa an kashe wasu mutane uku tare da jikkata jami'an 'yan sanda 60 a wani tashin hankali a birnin Bangalore na Kudancin Indiya.

Lamarin ya afku ne a lokacin gudanar da wata zanga-zanga da Musulmai suka yi game da wani shafin Facebook da ya wallafa kalaman batanci ga fiyayyen hallita Annabi Muhammadu.

Sashin Hausa ta BBC ta ruwaito cewa an yi harbe-harben ne bayan da dubban mutane suka kewaye gidan wani dan siyasar yankin wanda dan uwansa ne ya wallafa kalaman batancin.

Masu zanga-zangar sun rika yin jifa da duwatsu tare da banka wa motoci wuta.

Zanga-zangar yi wa Annabi batanci: An kashe mutum 3 a kasar Indiya
Zanga-zangar yi wa Annabi batanci: An kashe mutum 3 a kasar Indiya Hoto: Times of India
Asali: UGC

An tattaro cewa an sanya dokar tabaci a yankin yanzu haka, sannan dan siyasar ya wallafa wani sakon bidiyo, inda ya nemi jama’a su sanya zukatansu a inuwa.

'Yan sanda sun kama mutumin tare da masu zanga-zanga guda 110.

Kwamishinan 'yan sandan birnin, Kamal Pant ya ce 'yan sanda akalla 60 aka jikkata ciki har da manyan jami'ansu a daren Talata.

An saka dokar hana fita a unguwannin 'yan sanda biyu da ke birnin, a cewarsa.

A wani labari kuma, wata kotun shari'a ta yankewa matashin mawaki mai shekaru 30 hukuncin kisa ta hanyar rataya sakamakon batanci da yayi ga Annabi Muhammadu SAW.

Kotun da ke zama a Hausawa Filin Hockey wacce ta samu shugabancin Khadi Muhammad Ali Kani, ya yanke hukuncin bayan kama Sharif dumu-dumu da laifi.

Duk da cewar 'yan jarida kadan da jami'an tsaro aka bari suka shiga kotun, Daily Trust ta gano cewa laifin ya kusan suma bayan da alkalin ya yanke hukuncin.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an saka jami'an tsaro birjik a farfajiyar kotun.

An gurfanar da wanda ake zargin ne a kan batanci ga Annabi, wanda ya ci karo da sashi na 382, sakin layi na 6.

Kamar yadda bayanin da maiyarmu ta gano, wanda aka kaman ya yi wallafar ne a manhajar WhatsApp a ranar 28 ga watan Fabrairu, 2020 inda ya kira Annabi da Mushrik.

Dan sanda mai gabatar da kara, Sifeta Aminu Yargoje, ya sanar da kotun cewa an yi wannan wallafar ne don saka wani nau'in rashin jin dadi a tsakanin Musulmin jihar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel