Gbajabiamilla ya na nema ya rufe barnar da wasu su ka yi a NDDC – ‘Yan PDP

Gbajabiamilla ya na nema ya rufe barnar da wasu su ka yi a NDDC – ‘Yan PDP

‘Ya ‘yan jam’iyyar PDP a majalisar wakilan tarayya sun fito su na zargin kakakin majalisa, Femi Gbajabiamila, da kokarin bizne gaskiya a binciken hukumar NDDC.

‘Yan majalisar su na ganin cewa shugabansu ya na yunkurin rufa asiri ga wasu da su ka amfana da kwangiloli a hannun ma’aikatar NDDC mai kula da yankin Neja-Delta.

Jaridar Daily Trust ta ce ‘yan adawar sun jefi Femi Gbajabiamila da wannan zargi ne kwanaki kadan bayan Ministan Neja-Delta, Godswill Akpabio, ya bayyana a majalisa.

Da ya bayyana gaban kwamitin da ke binciken zargin badakala a NDDC, Sanata Godswill Akpabio ya ce akwai wasu ‘yan majalisa da su ke cin moriyar kwangilolin ma’aikatar.

‘Yan majalisar da ke karkashin PDP sun jefi Gbajabiamila da wannan zargi ne ta bakin shugabansu, Kingsley Chinda wanda ya aika takarda a ranar 2 ga watan Agusta.

KU KARANTA: NDDC ta kashe N2b wajen harkar yada labarai a cikin ‘yan watanni

Gbajabiamilla ya na nema ya rufe barnar da wasu su ka yi a NDDC – ‘Yan PDP
Majalisar wakilan tarayya
Asali: Twitter

Kingsley Chinda ya ce sun yi mamaki da su ka ji wasu su na neman hana mai girma Minista watau Godswill Akpabio jawabi a lokacin da ya ke gaban kwamitin majalisa.

Takardar ta ce: “Dole ta sa mu ka rubuto maka budaddiyar wasika, mu na rokon ka dauki matakin gaggawa ka kare darajar majalisar wakilai daga zubewa a idon jama’a.”

“Babu shakka a matsayinka na wanda ya ke cikin ‘yan majalisar da su ka fi dadewa tun 1999, ka san cewa majalisa ta na fuskanntar matsaloli; daga ciki har da kallon da ake yi mana.”

Ya ce: “Abubuwan da su ka faru kwanan nan musamman wajen binciken da aka yi a karkashinka, sun nuna cewa darajar majalisar wakilai ya na kara sauka kasa.”

Chinda ya ce abin takaici ne a idanun da-daman ‘Yan Najeriya, an ga yadda aka fito ana zargin wasu ‘yan majalisa da aikata ba daidai ba, ba tare da an dauki mataki ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel