Majalisar Tarayya: Mun gayyaci Ma’aikatu sun yi banza da mu, za mu je gaban Buhari

Majalisar Tarayya: Mun gayyaci Ma’aikatu sun yi banza da mu, za mu je gaban Buhari

‘Yan majalisar wakilan tarayya sun ce za su kai karar hukumomi da ma’aikatun gwamnatin tarayya da su ka ki karrama gayyatar da su ka yi masu.

Majalisa ta yanke cewa za ta kai kara ne gaban mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari.

A zaman da ta yi ranar 5 ga watan Agusta, 2020, domin gabatar da wani bincike, majalisar wakilan ta ce za ta kai maganar rashin da’ar zuwa fadar shugaban kasa.

‘Yan majalisar za su bukaci shugaba Muhammadu Buhari ya tursasawa jami’an gwamnati su halarci zaman da ake so ayi da su domin samun karin haske a bincikensu.

Kwamitin da ke sa ido a kan kudin gwamnati a majalisar wakilan Najeriya ya bayyana wannan kamar yadda jaridar The Cable ta fitar da rahoto a ranar Laraba.

Wannan kwamiti ya na binciken saida wasu kadarorin gwamnati da aka yi ba tare da bin ka’ida ba.

KU KARANTA: An tsige Mataimakin Shugaban Majalisar Edo

Majalisar Tarayya: Mun gayyaci Ma’aikatu sun yi banza da mu, za mu je gaban Buhari
Majalisar Wakilan Tarayya Hoto: Reps
Asali: Facebook

Daga cikin wadanda su ka watsawa majalisar kasa a ido akwai babban bankin CBN na kasa, hukumar bada agajin gaggawa na NEMA da kuma kamfanin man NNPC.

Haka zalika kwamitin ya ce shugabannin hukumomin gwamnatin tarayya na NPA, BPE da kuma PEF sun ki halartar zaman da majalisa ta bukaci ta yi da su.

Shugaban wannan kwamiti, Hon. Wole Oke, ya nuna rashin jin dadinsu game da yadda wadannan jami’an gwamnati su ka yi banza da gayyatar da aka aika masu.

Oke ya bukaci Akawun majalisar wakilai ya aikawa shugaban kasa Muhammadu Buhari takardar korafi ya sanar da shi game da wannan lamari.

‘Dan majalisar ya bada umarni cewa takardar ta bi ta ofishin sakataren gwamnatin tarayya, ana neman fadar shugaban kasa ta tursasawa jami’an su amsa goron gayyatar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel