Zaben Edo: Buhari ya gayyaci Ize-Iyamu yayinda ake shirin fara kamfen

Zaben Edo: Buhari ya gayyaci Ize-Iyamu yayinda ake shirin fara kamfen

Babban jigon jam'iyyar APC, Sanata Bola Ahmed Tinubu, shugaban majalisar dattawa, Dr. Ahmad Lawan, 'yan majalisar dattawa, gwamnonin APC da kuma jiga-jigan jam'iyyar za su hadu a Benin.

Za su hadu ne a babban birnin na jihar Edo a ranar Asabar mai zuwa domin fara yakin neman zaben gwamnan jihar.

Daga cikin shirye-shiryen kamfen din, shugaba Muhammadu Buhari ya gayyaci Fasto Ize-Iyamu, dan takarar kujerar gwamnan don ganawa ta musamman a fadarsa da ke Abuja.

Dan takarar, wanda tuni ya hallara a Abuja don taron, ya fara ganawa da wasu daga cikin mambobin kwamitin kamfen dinsa a daren Litinin.

Wadanda suka halarci taron sun hada da tsohon shugaban majalisar dattawa, Dr. Ken Nnamani, Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas.

Harda Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Kano, Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo da ministan kula da harkokin yankin Neja Delta, Sanata Godswill Akpabio da sauransu.

Edo 2020: Tinubu, Lawan da gwamnonin APC za su halarci kamfen
Edo 2020: Tinubu, Lawan da gwamnonin APC za su halarci kamfen Hoto: The Guardian
Asali: UGC

"Daga cikin shirye-shiryen fara yakin neman zaben a Benin a wannan Asabar, mambobin kwamitin sun samu ganawa da Fasto Osagie Ize-Iyamu a ranar Litinin don fara shirin.

"Shugaban kasar ya umarci dukkan gwamnonin APC da su halarci gangamin. Shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan, zai jagoranci mambobin majalisar dattawa don kamfen din," wani mamba ya sanar da jaridar ThisDay.

Majiyar ta ce shugaba Buhari ba zai samu halartar taron ba saboda kiyaye dokokin annobar kork a amma zai samu wakilcin manyan jami'an gwamnati.

KU KARANTA KUMA: Abdulaziz Yari ya jawo matsalar APC a Jihar Zamfara ba ni ba – inji Kabiru Marafa

A wani labarin kuma, mun ji cewa wasu mambobin jam'iyyar PDP karkashin inuwar wata kungiyar masu ruwa da tsaki ta jihar Edo, ta mika korafi ga hukumar yaki da rashawa.

'Ya'yan jam'iyyar sun nemi hukumar da ta binciki Gwamna Godwin Obaseki a kan zarginsa da ake da waskar da wasu makuden kudade.

Sun bukaci da a binciki gwamnan a kan wata kwangilar da ya bai wa kamfaninsa mai suna Afrilnvest Ltd.

Amma mai bada shawara ga Obaseki a fannin yada labarai, Crusoe Osagie, ya ce wannan korafin sharri ne wanda jam'iyyar APC ke shiryawa don bata sunan gwamnan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel