Abdulaziz Yari ya jawo matsalar APC a Jihar Zamfara ba ni ba – inji Kabiru Marafa

Abdulaziz Yari ya jawo matsalar APC a Jihar Zamfara ba ni ba – inji Kabiru Marafa

Tsohon sanatan Najeriya, Kabiru Garba Marafa, ya ce bai kamata a rika zargin shi a game da rashin nasarar da jam’iyyar APC ta samu a jihar Zamfara ba.

A ranar Talata, 4 ga watan Agusta, 2020, Kabiru Garba Marafa, ya yi hira da jaridar Daily Trust inda ya shaida cewa ba shi ya fara shigar da karar jam’iyya a kotu ba.

Kabiru Garba Marafa wanda ya wakilci yankin Zamfara ta tsakiya a majalisar dattawa sau biyu ya ce bangaren Abdulaziz Yari ne su ka fara zuwa kotu a jihar Zamfara.

A dalilin wannan kara da aka kai kotu, jam’iyyar APC ta rasa kujerar gwamna, Sanatoci uku, da ‘yan majalisar wakilai bakwai da kuma kujerun ‘yan majalisar dokoki 24.

A karshe, wadannan kujeru 35 (har da ta mataimakin gwamna) sun fado hannun jam’iyyar PDP a bagas.PDP ce jam’iyyar da ta zo ta biyu a duka zabukan da aka yi a Zamfara.

Sanata Marafa ya ce: “Shi (Yari) ya roki kotu ta amince da zaben fitar da gwanin da ya shirya, kuma a tursasawa hedikwatar APC ta amince da sakamakon zaben bogin, sai ta aikawa hukumar INEC domin a yarda ‘yan takararsu su shiga babban zabe.”

KU KARANTA: Oshiomhole ya ce taka wasu manya da ya yi ya ci shi a rikicin APC

Abdulaziz Yari ya jawo matsalar APC a Jihar Zamfara ba ni ba – inji Kabiru Marafa
Sanata Kabiru Marafa da Bukola Saraki Hoto: NASS
Asali: Twitter

Ya ce da farko, Yari ya yi nasara babban kotun jihar Zamfara ta amince da duka bukatun na sa.

“Sai mu ka tafi kotun daukaka kara da ke Sokoto, mu na kalubalantar shari’ar da aka yi. Duka Alkalai uku na babban kotun su ka ruguza hukuncin da aka yi a kotun (Zamfara).”

Marafa ya ce: “Ganin bai gamsu ba, Yari ya daukaka kara zuwa kotun koli, a nan babban kotun kasar, bayan ta amince da hukuncin kotun daukaka kara, ta ce daukacin kuri’un da APC ta samu ba su da amfani, kuma ta yi umarni a biya mu Naira miliyan goma.”

“To a nan wanene ya bata ruwan? Wa ya jawo matsalar? Ina tambayarku? Yaushe kare kai a kotu ya zama laifi a kasar nan? Marafa ya ke tambaya?

A gefe guda kuma, shugaban APC na Zamfara, Lawali M. Liman ya ce Kabiru Marafa ne ya jawo masu matsala a zaben 2019.

Alhaji Liman ya ce sun ci zabe tsaf, amma Marafa a lokacin ya na Sanatan jam'iyyar APC, ya kai kara a kotu, wanda a dalilin haka ne PDP ta karbe duka kujerunsu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel