Oshiomhole: Wasu manya da na taka su ka sa aka tsige ni daga Shugaban Jam’iyya

Oshiomhole: Wasu manya da na taka su ka sa aka tsige ni daga Shugaban Jam’iyya

- Adams Oshiomhole ya yi magana game da dalilin rasa kujerar shugaban jam’iyyar APC

- Tsohon gwamnan ya ce an tsige shi ne saboda ya bi ta kan wasu kusoshin jam’iyyar

- Oshiomhole ya ce bai yi da-na-sanin aikata abin da ya aikata a lokacin da ya ke ofis ba

A makon nan ne tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole, ya bayyana ainihin abin da ya jawo masa rasa kujerar da ya ke kai kwanaki.

Da ya ke magana a ranar 3 ga watan Agusta, 2020, Adams Oshiomhole ya ce ya bi ta kan wasu jiga-jigan APC ne a lokacin da ya ke rike da jam’iyyar mai mulki.

Oshiomhole ya yi wannan bayani ne yayin da aka yi hira da shi a gidan talabijin Arise News.

Da ya ke amsa tambayoyin a shirin safiyar da aka gabatar, Oshiomhole ya ce bai yi nadamar abin da ya faru ba, asali ma ya ce da zai samu wata dama, zai sake yin abin da ya yi.

Ya ce: “Kwarai, na san cewa idan ka taba wasu manya, za su dawo su yake ka, amma dama ban taba tunanin cewa zan zama shugaban jam’yya na har abada ba.”

KU KARANTA: NEC: Buhari ya bada shawarar a ruguza Majalisar Oshomhole

Oshiomhole: Wasu manya da na taka su ka sa aka tsige ni daga Shugaban Jam’iyya
Adams Oshiomhole
Asali: Depositphotos

Bayan an ruguza majalisar NWC ta Adams Oshiomhole, ya rungumi kaddara, ya ce: “Na yanke hukuncin ba zan kalubalanci matakin da aka dauka ba ne saboda biyayya ta.”

Tsohon gwamnan na jihar Edo ya kara da cewa: “Duk abin da ya faru a baya, ya zama tarihi, kuma ba zan iya yin abubuwa daban da yadda na yi ba.”

“Amma bari in tabbatar maka cewa ban yi da-na-sanin komai da mu ka yi ba, domin ba za ka iya canza Najeriya ba tare da ka taba wasu manya ba.” Inji sa.

Oshiomhole ya ce: “Ba ni nadamar komai a game da ruguza majalisar NWC wanda hakan ya kawo karshen wa’adi na. ‘Yan Najeriya su na so ne su ga an yi abubuwa dabam.”

Kwamred Oshiomhole ya rasa kujerar shugaban jam’iyya na kasa ne bayan majalisar koli ta APC watau NEC ta sauke shugabannin jam’iyyar a taron da ta yi a watan Yuli.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel