Buhari, Osinbajo da shugabannin tsaro sun shiga ganawa

Buhari, Osinbajo da shugabannin tsaro sun shiga ganawa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shiga taro da shugabannin tsaron Najeriya sakamakon hauhawar rashin tsaro a fadin kasar nan.

Baya ga shugaba Buhari, sauran wadanda suka halarci taron sun hada da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Ibrahim Gambari.

Sauran sun hada da mai bada shawara a kan tsaron kasa, Babagana Monguno da wasu ministoci.

Shugabannin sojin kasa, na ruwa, na sama, 'yan sanda, jami'an tsaro na farin kaya da kuma sashen sirri na rundunar soji duk sun halarci taron.

Wannan taron na faruwa ne bayan kusan mako daya da wasu miyagu suka kai wa tawagar Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno hari.

Buhari, Osinbajo da shugabannin tsaro sun shiga ganawa
Buhari, Osinbajo da shugabannin tsaro sun shiga ganawa Hoto: Fadar Shugaban kasa
Asali: Twitter

Amma kuma Zulum ya ce wannan harin ba Boko Haram bane suka kai masa shi. Sojoji ne suka kai masa.

Harin ya zo ne bayan kwana daya da tagwayen bama-bamai suka tashi a garin Maiduguri wanda 'yan Boko Haram suka tada.

Baya ga mayakan Boko Haram, 'yan bindigar daji na cin karensu babu babbaka a jihohin arewa maso yamma inda suke kashe jama'a tare da garkuwa da wasu.

KU KARANTA KUMA: Da izinin mahaifinsu na dinga musu fyade har suka yi ciki - Wanda ake zargi

Taron shugabannin tsaron da ake a yau Talata, ana tsammanin zai kawo maslaha a kan matsalar tsaro da ta addabi kasar nan.

A gefe guda, gwamnonin jihohi 36 na fadin tarayya, sun bayyana damuwa dangane da yadda lamari na rashin tsaro ke ci gaba da tabarbarewa a kasar.

Sanadiyar hakan ne ya sanya gwamnonin karkashin kungiyarsu ta NGF, suka yanke shawarar garzaya wa har fadar shugaban kasa domin gudanar da zama na musamman da shugaba Muhammadu Buhari.

Gwamnonin bayan zaman kwamitinsu na tsaro, sun yanke shawarar kai wa shugaban kasa Buhari koken al'ummarsu dangane da hali na rashin tsaro da ya ke kara tsananta.

Gwamnonin yayin bayyana damuwa dangane da harin da ake zargi 'yan Boko Haram sun kai wa ayarin motocin gwamna Babagana Zulum na jihar Borno, sun kuma nuna bacin rai a kan tabarbarewar tsaro duk da kokarin gwamnatin tarayya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel