An kama wasu Malaman asibiti da zargin saida jariri a Jihar Katsina

An kama wasu Malaman asibiti da zargin saida jariri a Jihar Katsina

Wasu mata uku, daga ciki har da masu aikin jinya biyu sun shiga hannun dakarun ‘yan sanda na reshen jihar Katsina da laifin sace jaririya.

Jaridar Punch ta rahoto cewa ana zargin wadannan mata da yunkurin sace wata jaririya da aka haifa, aka bar ta a wani asibitin kudi da ke cikin jihar Katsina.

Kamar yadda ‘yan sanda su ka bayyana, wata Shamsiya Sani da ke unguwar Dandagoro, Katsina, ce ta haifi jaririya a ranar 25 ga watan Yuli, 2020.

Wannan mata ta tsere ta bar yarinyar da ta haifa kwance a gadon asibiti dauke da takarda da ke nuna cewa ta samu cikinta ne ba tare da mijin aure ba.

Jami’an ‘yan sanda sun bayyana cewa ma'aikatan jinya; Misira Tijani da Grace Ejigu sun dauke wannan jaririya sun saidawa wata Eucharia Onyema.

Yanzu haka an kama duka wadanna mata uku da ake zargi da satar jaririyar, an kuma gabatar da su a babban ofishin ‘yan sanda ke Katsina a jiya Litinin.

KU KARANTA: Wani Sarkin da ya ke da hannu a fashi da makami ya shiga hannu

Kakakin ‘yan sandan jihar, SP Gambo Isah ya ce direban da wadannan mata su ka yi haya ne ya kawo kararsu gaban ofishin ‘yan sanda da ke Sabongari.

Wannan direba ya ji abin da matan su ke tattaunawa, daga nan ya yi wuf ya sanar da jami’an tsaro.

“Jaririyar ta na hannun sashen walwala da jin kai na ma’aikatar matasa da cigaban al'umma inda ta ke samun kula a halin yanzu.” Inji Isah a madadin jami’an ‘yan sanda.

A na su bangaren, malaman asibitin sun musanya zargin cewa sun saida jaririyar ne, sun ce sun damkawa Eucharia Onyema ne a matsayin taimakon rai.

“Mun dauki wannan mataki ne domin mu taimaka. Ba saida jaririn mu ka yi ba. Kuskurenmu daya shi ne da ba mu sanar da hukumar asibiti kafin mu yi wannan ba.” Inji Tijjani.

Ita ma Onyema ta ce ba ta biya malaman jinyar ko sisi ba, ta ce ta karbi jaririyar ne domin ba ta taba haihuwa ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng