IBA: Famuyiwa Olushola tayi nasara a gasar kungiyar Lauyoyi
Wata ‘daliba da ke aji uku a tsangayar ilmin shari’a a jami’ar Ilorin, Famuyiwa Olushola ta lashe wata gasar farko da kungiyar lauyoyi ta Duniya ta shirya.
Kamar yadda jami’ar tarayyar da ke Ilorin, jihar Kwara, ta bayyana a wata takarda da ta fitar, Miss Famuyiwa Olushola ta yi nasara ne a gasar Vlogging da aka tsara.
Wata babba a kungiyar Lauyoyin Duniya ta IBA, Anna Toth ta aikowa Olushola takardar nasarar da ta sa wa hannu daga babban birnin Landan a kasar Ingila.
Wannan daliba ce aka zaba a matsayin ta farko a harkar Vlogging na rukunin daliban da ke karantar ilmin shari’a a gasar kungiyar IBA.
Takardar ta ce: “Kungiyar IBA ta shirya wasan Vlogging na farko a tarihi domin kananan Lauyoyi da daliban ilmin shari’a domin su bada gudumuwarsu a game da annobar cutar COVID-19 da shari’a.”
KU KARANTA: Najeriya ta kashe N500m wajen ciyar da 'Yan makaranta a lokacin kulle
An aikowa dalibar wannan takarda ne a ranar 28 ga watan Yuli, 2020. Daga cikin kyautar da ta samu shi ne yafe mata kudin rajista da kungiyar IBA na tsawon shekara biyu.
Bayan haka Famuyiwa Olushola ba za ta biya ko sisi daga cikin kudin zuwa taron Lauyoyi na Duniya da kuma taron karawa juna sani da za ayi a shekarar 2021 ba.
Sauran kyaututtukan da ta samu sun hada da samun tikitin zuwa da dawowa na jirgin sama domin halartar wadannan tarurruka, kungiyar ta kuma daukewa Budurwar kudin otel.
Olushola ta yi farin ciki da aka zabe ta a matsayin wanda ta lashe wannan kyauta. Hukumar dillacin labarai na kasa ta rahoto dalibar ta na cewa wannan kyauta za ta taimaka mata.
Kwanaki kun ji cewa Rukaiya El-Rufai ta samu aiki da kamfanin PricewaterhouseCoopers a Najeriya. Babu wata ‘Yar Arewa da ta taba aiki da wannan kamfani a tarihi.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng