Abinda yasa Atiku, Saraki da Kwankwaso ba za su koma APC ba

Abinda yasa Atiku, Saraki da Kwankwaso ba za su koma APC ba

Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasa, tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki da tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ba su tunanin komawa jam'iyyar APC, hadimansu suka sanar da jaridar Daily Trust a jiya Litinin.

Bayan komawar Dogara jam'iyyar APC tare da Sanata Barnabas Gemade, jam ta yi kira ga wadanda suka koma PDP da su dawo gida.

A wata takarda da ta fito daga hannun mataimakin sakataren yada labarai na jam'iyyar, Yekini Nabena, ya ce jam'iyyar a shirye take don karbar sabbin mambobi da kuma wadanda suke son dawowa.

Amma da aka tuntubi mataimaki na musamman ga Atiku Abubakar a fannin yada labarai, Paul Ibe ya sanar da cewa uban gidansa ba zai taba komawa "jirgin ruwan mai nitsewa ba".

“Ba gaskiya bane, wannan jam'iyyar na yi ne don birkita tunanin jama'a ko don gazawar da tayi tare da kasa cike alkawurran da ta daukarwa jama'a," yace.

"Mulkinta a shekaru biyar da suka gabata ya bar jama'a cikin kangi. Dokokinsu ya mayar da mutane marasa aikin yi.

"Komawa APC tamkar shigewa wuta ne da hankalin mutum," ya kara da cewa.

Abinda yasa Atiku, Saraki da Kwankwaso ba za su koma APC ba
Abinda yasa Atiku, Saraki da Kwankwaso ba za su koma APC ba Hoto: The Cable
Asali: Facebook

Hakazalika, hadimin Saraki wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce uban gidansa na ketare tare da iyalansa kuma ya bayyana wannan zance a matsayin shirme.

"Suna son janye hankalin jama'a ne daga rikicin jam'iyyar da gazawar mulkinsu. Dogara yana da matsala da gwamnansa ne. Babu wani tsari tsakaninsa da Saraki na komawa APC. Jam'iyyar a halin yanzu babu mai sonta," yace.

A bangaren Kwankwaso kuwa, Kwamared Aminu Abdussalam, ya ce babu dan siyasa mai tunani da zai koma APC "wacce ke shirin tarwatsewa."

KU KARANTA KUMA: Da izinin mahaifinsu na dinga musu fyade har suka yi ciki - Wanda ake zargi

"Gaskiyar abinda na sani shine Injiniya Rabiu Kwankwaso dan PDP ne. Amma kuma ta yaya kuke tsammanin mutum mai tunani zai koma APC?

"APC na shirin rugujewa ne kuma ta tarwatse a jihar Kano. Akwai illolin da suka yi wa kansu kuma babu yadda za su warke. Sun lalata koma tare da assasa rashin tsaro.

"A shekaru biyar da suka gabata na mulkinsu, 'yan Najeriya basu san komai ba banda wahala," Abdussalam yace.

A wani bangare na daban, shugabannin jam'iyyar APC na Bogoro, Tafawa Balewa da karamar hukumar Dass sun kwatanta komawar Dogara APC da babban ci gaba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel