Masu jarrabawar WASSCE za su gamu da kicibis a Ranakun Juma’a a bana - MURIC

Masu jarrabawar WASSCE za su gamu da kicibis a Ranakun Juma’a a bana - MURIC

Kungiyar MURIC da ke kare hakkin addinin musulunci ta soki sabon jadawalin jarrabawar WASSCE ta kammala karatun sakandare da aka fitar da shi.

Hukumar WAEC mai tsara jarrabawar WASSCE ta shirya cewa za a fara jarrabawar bana a ranar Talata, 17 ga watan Agusta, amma jarrabawar za ta fado har a ranakun Juma’a.

MURIC ta fitar da jawabi ne ta bakin shugabanta, Farfesa Ishaq Akintola a safiyar ranar Litinin.

Shugaban MURIC ya ce a sabon jadawalin da WAEC ta fitar kwanan nan, wasu jarrabawowin za su fado a daidai lokacin da musulman Najeriya su ke yin sallar Juma’a.

Farfesa Ishaq Akintola ya zargi hukumar jarrabawar da jefa masu rubuta WASSCE cikin tsaka mai wuya, na yin zabi tsakanin jarrabawar kammala sakandare da kuma ibadarsu.

Ya ce: “Akwai akalla kicibis uku da za a samu na jarrabawar da lokutan sallar Juma’ar musulmai: ranar 14 ga watan Agusta, 21 ga watan Agusta, da 4 ga watan Satumba.”

KU KARANTA: Zaman lafiya shi ne Kudu su yi mulki bayan Buhari - Matasan Arewa

Masu jarrabawar WASSCE za su gamu da kicibis a Ranar Juma’a a bana - MURIC
Shugaban MURIC, Farfesa Ishaq Akintola
Asali: Facebook

Masu rubuta jarrabawar adabin turanci da kimiyyar lafiya su na cikin wadanda za su samu wannan cin karo a shekarar nan kamar yadda jadawalin WAEC ya nuna.

Farfesa Akintola ya ce idan aka tafi a haka, za a kuntatawa musulmai, kuma za a iya samun matsala.

Akintola ya ce ba a yi la’akari da musulman dalibai wajen tsara jarrabawar ba, sannan ya ce jadawalin zai iya tunzura al’umma tare da zargin hukumar da bangaranci.

“Danyen aikin masu kokarin jawo fitina ne. Boyayyar dabarar makiya addini ce da aka lullube da kiyayya da rashin adalci. Duk da kokarin da mu ke yi domin hana aukuwar irin wannan”

Wannan kungiya da ke kare hakkin musulman kasar ta ce dole a ba musulmai sa’o’i uku a ranar Juma’a domin su yi sallah duk da cewa ana rubuta wannan jarrabawa.

“Sakonmu ga WAEC mai sauki ne kuma kai tsaye: Ku canza jadawalinku, kuma ku daina tunzura musulmai daga yanzu.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel