Jami’an ‘Yan Sanda 30 su ke lura da Kauyuka kimanin 100 a Katsina – Masari

Jami’an ‘Yan Sanda 30 su ke lura da Kauyuka kimanin 100 a Katsina – Masari

Gwamnan jihar Katsina, Rt. Hon. Aminu Bello Masari, ya ce manyan jami’an ‘Yan sanda 30 rak su ke ba daruruwan kauyuka tsaro a fadin jiharsa.

Gwamnan ya bayyana wannan ne a lokacin da ya yi bikin babbar sallah tare da jami’an tsaron da ke filin daga a Katsina, ya ce jihar ta na fama da karancin jami’ai.

Mai girma gwamnan ya ce ya na kokarin ganin an yi wa dokokin kasa garambawul ta yadda kananan hukumomi za su iya magance matsalar da ake fama da ita.

Aminu Bello Masari ya ce ‘yan bindiga sun saje da mutanen cikin karkara da kauyaka don haka ya ke wahala a iya banbamce tsakanin nagari da miyagun.

Idan aka ba kananan hukumomi damar yakar ‘yan bindiga, gwamnan ya na ganin za a samu saukin rashin tsaro, wanda har yanzu ya ki ci, ya ki cinyewa a Katsina.

“Wannan zai taimakawa kokarin samar da jami’an tsaro na cikin gida, yayin da ake magance matsalar karancin ‘yan sanda a kananan hukumomi, inda ake da kimanin jami’an ‘yan sanda 30 ga kauyuka 100.”

KU KARANTA: Bam ya tashi da wasu yara a Jihar Katsina

Jami’an ‘Yan Sanda 30 su ke lura da Kauyuka kimanin 100 a Katsina – Masari
Gwamnan Katsina Aminu Masari
Asali: UGC

Masari ya kara da cewa: “Ko da jami’an tsaro sun lallasa duka ‘yan bindigan, wasu sababbin zubin miyagu za su bayyana a madadinsu, saboda rashin gwamnati da isassun jami’an tsaro.”

“’Yan bindigan sun cudanya da al’umma, saboda haka wani lokaci zai yi wa sojojin sama ko na kasa wahalar banbamcesu da sauran mutanen gari yadda ba za a kai harin kan mai uwa da wabe ba.”

“Dole mutanen gari su daina ba su goyon-baya, ko bayanai, ko kuma su zama wurin fakewar wadannan mugaye.”

A na sa bangaren, shugaban hafsun sojin sama, Sadique Abubakar ya ce za a tura jiragen UAVs masu tuka kansu domin maganin ‘yan bindiga zuwa jihohin Katsina da Zamfara.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel