Kungiyoyi sun rubutawa Buhari takarda, su na so a binciki Abubakar Malami

Kungiyoyi sun rubutawa Buhari takarda, su na so a binciki Abubakar Malami

Wasu kungiyoyi masu zaman kansu sun yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ya binciki ministan shari’a, Abubakar Malami game da wasu zargi da ke kansa.

Jaridar The Cable ta ce wadannan kungiyoyi su na zargin akwai hannun babban lauyan gwamnatin Najeriya, Abubakar Malami SAN a wasu badakala 14 da aka tafka na rashin gaskiya.

A wata takarda da aka aikawa shugaban kasa a karshen makon jiya, kungiyoyin sun jefi ministan shari’an da zargin satar kudi, amfani da kuma kujerarsa wajen yin ba daidai ba.

Shugaban kungiyoyin CSNAC, CACOL da SayNoCampaign; Olanrewaju Suraju, Debo Adeniran, da Ezenwa Nwagwu su ka sa hannu a wannan takarda da aka aikawa shugaban kasa.

Mista Olanrewaju Suraju mai jagorantar kungiyar CSNAC mai yaki da rashin gaskiya a Najeriya, ya na da kananan kungiyoyi 150 a karkashinsa.

Kungiyoyin nan sun nemi Ministan ya yi murabus domin a samu damar gabatar da cikakken bincike. Shugabannin kungiyoyin sun ce ya kamata shugaban kasa ya dauki mataki.

KU KARANTA: Shekara 1 babu labari da sace wani ‘Dan adawa a Najeriya

Kungiyoyi sun rubutawa Buhari takarda, su na so a binciki Abubakar Malami
AGF Abubakar Malami
Asali: Facebook

“Ko dai ayi (bincike) yanzu, ko kuma ba za ayi ba har abada. Akwai zargin aikata rashin gaskiya masu karfi a kan Abubakar Malami da hujjoji kamar rana a lokacin azahar.”

Jawabin ya kara da cewa: “Shugaba Muhammadu Buhari ya dauki mataki yanzu.”

“Mun jero laifuffukan ne bayan mun tattaro zargin da ke kan babban lauyan gwamnatin kasar. Dole shugaban kasa ya dauki mataki ba tare da wata-wata ba.”

Kungiyoyin sun ce rahotannin da su ka samu ya tada masu hankali, sun zargi Malami da rashin bin dokar kasa wajen aiki. A cewarsu, wannan abin jawowa Buhari suka ne.

Daga cikin zargin da aka ambata har da batun cewa AGF ya bada umarnin saida wasu ganguna da ke dauke da danyen man Najeriya da aka sace, wanda hukumar EFCC ta ke bincike.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel