Karamin soja ya budewa babban soja wuta a jihar Borno

Karamin soja ya budewa babban soja wuta a jihar Borno

Wani karamin soja da ake zargin ya na fama da ciwon matsananciyar damuwa (depression) ya budewa wani babban soja a ranar Laraba. Babban sojan ya mutu nan take.

Jaridar The Nation ta rawaito cewa lamarin ya faru ne a jihar Borno kuma har yanzu rundunar soji ba ta saki bayanan sojan da aka harbe ba.

Shi kansa sojan da ya yi kisan ba a bayyana sunansa ba bayan sanin cewa karamin soja ne da ke aiki da bataliya ta 202 a karkashin rundunar soji ta 21 da ke Bama a jihar Borno.

Kanal Sagir Musa, mukaddashin jami'in hulda da jama'a na rundunar soji, ya ce; "wani karamin soji da ke tare da bataliya ta 202 a runduna ta 21 da ke Bama a jihar Borno ya tubure da misalin da 10:30 na ranar 29 ga watan Yuli, 2020, tare da budewa babban soja wuta, lamarin da ya zama silar mutuwarsa.

"Ya bude ma sa wuta ne a lokacin da ya zo wurinsa shi kuma ya na magana a waya. An kama karamin sojan tare da fara gudanar da bincike. Yanzu al'amura sun koma daidai."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel