Za a sake kawo wasu hari a Kudancin Jihar Kaduna – ‘Yan Majalisa sun ce ayi hattara

Za a sake kawo wasu hari a Kudancin Jihar Kaduna – ‘Yan Majalisa sun ce ayi hattara

Wasu ‘yan majalisar wakilan tarayya daga yankin kudancin jihar Kaduna sun sanar da Duniya cewa akwai shirin da ake yi na kuma kai wa mazabunsu hari.

Wadannan ‘yan majalisa da su ke wakiltar mutanen kudancin Kaduna sun ce miyagu da makiyayan da ke yawo da makamai za su kawo farmaki a lokacin bikin sallah.

‘Yan majalisar tarayyar sun yi wannan bayani ne a gaban ‘yan jarida ranar Laraba a garin Abuja.

Honarabul Gideon Gwani ne wanda ya jagoranci tawagar ‘yan majalisar. Da ya ke amsa tambayoyin manema labarai, ya soki gwamnatin jihar ta Nasir El-Rufai.

Hon. Gwani ya yi tir da gwamna Malam Nasir El-Rufai na kin amincewa da kungiyar SOKAPU ta muutanen kudancin Kaduna, ya ce jama’a sun yarda da aikin kungiyar.

Sauran ‘yan majalisar da su ka yi masa rakiya wajen wannan jawabi sun hada da Nicholas Garba, Mukhtar Zakari; Gabriel Zock, da kuma Honarabul Amos Magaji.

‘Yan majalisar su na wakiltar yankin Kaura, Zagon Kataf/Jaba, Jema’a/Sanga, Kauru, da Kachia/Kagarko na jihar a majalisar tarayya.

KU KARANTA: An kama masu garkuwa da mutane 35 a Najeriya

Za a sake kawo wasu hari a Kudancin Jihar Kaduna – ‘Yan Majalisa sun ce ayi hattara
Malam Nasir El-Rufai Hoto: Gov Kaduna
Asali: Facebook

“Idan aka zo maganar tsaro a can, mutanenmu na su na ganin jami’an tsaro ba su yin abin da ya kamata. Wannan ya sa ake kai hari musamman a kan iyaka a lokacin da aka sa dokar hana fita.” Inji Hon. Gwani.

“A lokacin da aka kafa dokar hana zirga-zirga, abin da ke faruwa shi ne, ana samun tsaro a cikin birane, ba a samu hare-hare a gari, sai a kauyukan da ke kan iyaka.”

‘Dan majalisar ya ke cewa yanzu haka mutanen Kudancin Kaduna sun samu labari cewa wadanda su ka kawo hari a baya za su sake kawo farmaki a lokacin hutun sallah.

Kamar yadda Gwani ya yi ikirari, miyagun su kan sanar da jama’a niyyarsu kafin su kawo hari.

'Dan majalisar na Kaura ya ce: “Na fadawa DPO ya sanar da manyansa game da shirin harin, kuma ya dauki maganar da gaske. Amma har yanzu ana kawo hari.”

“Ya na da muhimmanci a sani, bayanai sun zo mana cewa za su kawo gagarumin hari a kudancin Kaduna lokacin hutun bikin sallah. Mu na kiran mutanenmu su sa ido.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel