Olounrinu: ‘Yan Najeriya su roki Bola Tinubu ya fito takarar Shugaban kasa

Olounrinu: ‘Yan Najeriya su roki Bola Tinubu ya fito takarar Shugaban kasa

Dipo Olounrinu wani tsohon ‘dan jam’iyyar PDP wanda yanzu na cikin manyan APC ya yi magana game da siyasar zaben 2023, inda ya ce Bola Tinubu ya dace ya zama shugaban kasa.

Honarabul Dipo Olounrinu ya ce masu sukar Asiwaju Bola Tinubu a kan 2023, su na yi masa hassada ne a game da irin nasarorin da ya samu a rayuwarsa da kuma tafiyar siyasa a kasa.

Olounrinu wanda ya rike kujerar majalisa a Legas, ya shaidawa Daily Trust cewa babu wani ‘dan siyasa a kasar nan da ya kama kafar tsohon gwamnan Legas Bola Tinubu.

A cewar Dipo Olounrinu “Jagoran na APC ya yi sanadiyyar da rayuwar dinbin mutane su ka yi tasiri a rayuwar miliyoyin jama’a”

Duk da wannan jita-jita da ya ke yawo, har yanzu Tinubu bai taba cewa ya na sha’awar mulki ba.

A game da Tinubu, Olounrinu ya ce: “Ban ga dalilin da zai sa ba za a ba shi dama ba.”

KU KARANTA: Sanata Udoedeghe ya fadawa ‘Yan APC dabarar lashe zaben 2023

Olounrinu: ‘Yan Najeriya su roki Bola Tinubu ya fito takarar Shugaban kasa
Bola Tinubu da Shugaban kasa Hoto: Twitter
Asali: Depositphotos

“Ba ka isa ka kaure abin da ya ke da kyau ba. Abu mai kyau, ya na da kyau ne kawai.”

Ya kara da cewa: “Wannan (Tinubun) mutum ne wanda ya ke da tarihi da nasaba.”

“Ana bukatar kwararrun mutane da su ka san aiki, su ka san rayuwa gaba daya, sun ga jiya sun ga yau. Wanda rayuwa ta yi masu kyau.” inji sa..

A cewarsa Tinubu ya nuna kwarewa a siyasa wajen yadda APC ta zama jam’iyyar da ke mulki a Najeriya, kuma duk mai nuna adawa garesa, hassada kurum ya ke yi masa.

Bayan nan Olounrinu ya tunawa jama’a yadda Bola Tinubu ya yi gwagwarmayar adawa a lokacin ya na gwamnan jihar Legas. Ya ce don haka babu wanda ya dace da mulki irinsa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel