Bunkasa tattalin arziki: Pantami ya lissafa aiyuka 6 da ma'aikatarsa za ta yi a jihohi 4

Bunkasa tattalin arziki: Pantami ya lissafa aiyuka 6 da ma'aikatarsa za ta yi a jihohi 4

Ministan sadarwa da bunkasa tattalin arziki ta hanyar fasahar zamani, Dakta Isa pantami, ya kaddamar da aiyuka 6 da aka kammala a karkashin sabon tsarin tattalin arziki na zamani.

Dakta Pantami, wanda ya wakilci shugaban kasa, Muhammadu Buhari, yayin kaddamar da aiyukan, ya ce zasu inganta tattalin arzikin Najeriya.

Ministan ya bayyana cewa kaddamar da sabbin aiyukan yana daga cikin manufofin gwamnatin shugaba Buhari na fadada hanyoyin shigowar kudi, tabbatar da tsaro, da kuma habaka bangaren fasahar sadarwa ta zamani (ICT).

An kaddamar da aiyukan ne ta hanyar fasahar yanar gizo mai amfani da karfin yanar gizo.

Aiyukan sun hada da wata makarantar gaba da sakandire a jihar Enugu, ofishin cibiyar sadarwa na yankin arewa maso yamma da ke Kaduna, da wata cibiyar sadarwa jama'a a jihar Katsina.

Sauran sun hada da wata bukkar fasahar sadarwa a Kaduna da wata takwararta a jihar Legas da kuma cibiyar sadarwa ta gaggawa a Kaduna.

Bunkasa tattalin arziki: Pantami ya lissafa aiyuka 6 da ma'aikatarsa za ta yi a jihohi 4
Pantami
Asali: Twitter

Ya ce aiyukan 6 sun karada kowanne bangare na bunkasa tattalin arzikin kasa ta hanyar amfani da tsarin dabarun sarrafa fasahar zamani a kasa (NDEPS).

DUBA WANNAN: Mata sun yi birgima a kasa tsirara yayin zanga - zanga a Kaduna

A cewarsa, shugaba Buhari ne ya kaddamar da shirin NDEPS a ranar 28 ga watan Nuwamba na shekarar 2019 bayan ma'aikatar sadarwa ta gabatar ma sa da bukatar hakan a matsayin daya daga manyan aiyukanta na zamanantar da tattalin arziki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel