Ana neman Kansila da mutum 13 a kan mutuwar Sarkin Garin Okobo

Ana neman Kansila da mutum 13 a kan mutuwar Sarkin Garin Okobo

A jihar Akwa-Ibom, jaridar Vanguard ta fitar da rahoto cewa jami’an tsaro su na neman wani Kansila da laifin kisan Mai garin Okobo a karamar hukumar Okobo.

Jaridar ta ce Kansilan da wasu mutane 13 ake nema a halin yanzu bisa zarginsu da ake yi da hannu a mutuwar wannan Basarake da ya bar Duniya a ranar Lahadi.

Mai magana da yawun bakin ‘yan sanda na jihar Akwa Ibom, CSP Frederick N-Nudam, ya ce ana zargin Kansilar Okobo, Nkereuwem John da hannu a mutuwar Mai garin.

Mista Nkereuwem John shi ne Kansilar rikon kwarya da ke lura da sha’anin kudi a karamar hukumar har zuwa lokacin da wannan abin takaici ya faru.

Frederick N-Nudam ya zargi Nkereuwem John da hada-kai da wani jagoran matasa mai suna Usong Morrison John wajen murkushe marigayi mai martaba.

Kakakin ‘yan sandan ya bayyana cewa Kwamishinan ‘yan sanda na Akwa Ibom, Imohimi Edgal, ya bada umarnin a cafke duk wadanda ake zargi da hannu a laifin.

KU KARANTA: An kama masu shirya fim din batsa

Ana neman Kansila da mutum 13 a kan mutuwar Sarkin Garin Okobo
Gwamna Emmanuel da wasu mutanen Akwa Ibom
Asali: Facebook

Jami’in tsaron ya ce su na zargin cewa Nkereuwem John da mutanesa sun kitsa wannan aiki ne domin su rama kisan wani matashi Aniefiok Mkpo-Abasi da aka yi masu.

Mkpo-Abasi wani shugaban matasa ne na karamar hukumar da ya mutu a gidan wani Walter Ukoh, Ana zargin na kusa da Marigayin da kashe Ukoh wajen daukar fansar gayya.

CSP N—Nudam ya zargi wadannan mutane da daukar doka a hannunsu. Bayan haka jami’in ‘yan sandan ya ce yanzu sun cafke mutane 15 da ake zargi su na da hannu a kisan.

N-Nduma ya ce ya kamata ace mutanen garin sun kawo kara gaban hukuma ne a lokacin da abin ya faru, a maimakon su nemi su kashe rai ba tare da hakkin jini ba.

‘Yan Sanda sun ce Kansilan sun kitsa yadda za su yi ta’adin ne bayan sun yi wani taro a majalisar Kauyen, daga nan su ka kashe Henry Esimeme da Sunday Walter Ukoh.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel