Charles Ude ya na so Alkali ya hana Ize-Iyamu takara a karkashin jam’iyyar APC

Charles Ude ya na so Alkali ya hana Ize-Iyamu takara a karkashin jam’iyyar APC

A ranar Laraba, 22 ga watan Yuli, 2020, Charles Ude, daya daga cikin ‘ya ‘yan jam’iyyar APC kuma Lauya a jihar Edo, ya shigar da kara a kan jam’iyyarsa da shugabanninta.

Mista Charles Ude ya kai kara a gaban babban kotun tarayya da ke zama a Abuja, ya na rokon Alkaki ya haramtawa Osagie Ize-Iyamu tsayawa takarar gwamnan jihar Edo.

A wannan kara da aka shigar mai lamba FHC/ABJ/CS/839/2020, Ude ya fadawa kotu cewa ba a bi ka’ida wajen tsaida Ize-Iyamu a matsayin ‘dan takarar jam’iyyar APC ba.

Osagie Ize-Iyamu ya samu tikitin APC ne a zaben fitar da gwani da aka yi kwanaki, hakan na nufin zai rikewa jam’iyyar tuta a zaben gwamna da za a yi a watan Satumba.

Lauyan ya ce hanyar da aka bi wajen tantance ‘dan takarar da kuma tsaida shi ya sabawa dokokin jam’iyya. A cewarsa akwai matsala tattare da kwamitocin da su ka yi wannan aiki.

Jaridar Vanguard ta rahoto Ude ya na mai cewa kotu ta dakatar da Adams Oshiomhole daga matsayinsa na shugaban jam’iyya a lokacin da aka dauki wannan matakai.

KU KARANTA: Shugabannin rikon kwaryar APC sun fara aikin dinke baraka

Charles Ude ya na so Alkali ya hana Ize-Iyamu takara a karkashin jam’iyyar APC
Fasto Osagie Ize-Iyamu
Asali: Twitter

Don haka ne ‘dan jam’iyyar ya bukaci kotu ta rusa takarar Fasto Osagie Ize-Iyamu domin kuwa duk doka ba ta san da zaman Oshiomhole a lokacin da aka yi zaben fitar da gwanin ba.

Mai karar ya tunawa kotu cewa Victor Giadom ne ainihin shugaban jam’iyyar APC a watan da ya gabata, kuma ya yi fatali da kwamitocin da su ka yi aikin fitar da ‘dan takara a jihar Edo.

Wadanda aka hada a cikin wannan kara a gaban kotun sun hada da jam’iyyar APC, Adams Oshiomhole, Victor Giadom, Hilliard Eta, hukumar INEC da Fasto Ize-Iyamu.

Wanda ya shigar da karar ya na tambaya ko shugaban da aka dakatar daga ofis zai iya gudanar da aikin shugaban jam’iyya na kasa, bayan nan sai ya bukaci a ruguza takarar Ize-Iyamu.

Har yanzu ba a sa ranar da kotu za ta zauna domin sauraron wannan kara ba. Kwanaki shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga ‘yan APC su janye duk karar da su ka shigar a kotu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel