Kaduna: 'Yan sanda sun yi babban kamu, sun kama 'yan bindiga 217

Kaduna: 'Yan sanda sun yi babban kamu, sun kama 'yan bindiga 217

Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta damke wasu mutum 217 da ake zargi da garkuwa da mutane, fashi da makami, satar dabbobi da sauran su.

Kwamishinan 'yan sandan jihar Kaduna, CP Umar Muri, wanda ya gurfanar wadanda ake zargin a ranar Laraba, ya bayyana bindigogi 43 kirar AK 47.

CP Muri ya ce wadanda ake zargin an kama su ne tsakanin ranar 29 ga watan Afirilu zuwa 22 ga watan Yuli, bayan sake duba tsarin tsaro da aka yi na jihar Kaduna.

Kamar yadda kwamishinan dan sandan yace, "bayan hakan, lamarin tsaron jihar Kaduna ya fara samun daidaituwa a kwanakin nan.

" Wannan na daga cikin sabbin tsare-tsaren tsaro da jihar ta zo da shi tare da taimakon sifeta janar na 'yan sandan Najeriya, Mohammed Abubakar Adamu.

"A yau ina farin cikin sanar da ku cewa a cikin makonnin kadan da suka gabata, rundunar ta damke wadanda ake zargi 217 a kan laifuka daban-daban da suka hada da fashi da makami, 'yan bindigar daji, garkuwa da mutane, satar dabbobi, fyade, balle shaguna, sata da sauran laifuka.

Kaduna: 'Yan sanda sun yi babban kamu, sun kama 'yan bindiga 217
Kaduna: 'Yan sanda sun yi babban kamu, sun kama 'yan bindiga 217 Hoto: The Cable
Asali: UGC

"A yayin bincike, an samo abubuwa da suka hada da: Bindigogi kirar AK47 43, harsasai 1,113, adduna 11, kwari da baka 1, gora 10 da almakashi 1.

"An samo kudi har N93,008,783 da kuma riyal 180,070. A cikin wannan lokacin an samo kudin jabu har $5,700,000. Euro 200,000, CFA 210,000 da N2,700,000 duk na jabu.

"Mun samo buhu 2,400 na abincin kaji da za su kai darajar N8,343,750, buhu 823 na shinkafa, motoci 10, babura 31, talabijin 15, shanu 833, tumaki 20, wayoyi 14, laptop 9, katin shaida na 'yan sanda na bogi 6, abun kashe gobara 2, buhu 48 na wiwi da wasu layu.

"Za ku yarda da ni cewa an samo wadannan kayayyakin ne sakamakon binciken da muka yi a cikin kankanin lokaci.

“Hakan na nuna ana samu nasarori masu tarin yawa," kwamishinan 'yan sandan yace.

Ya yi kira ga jama'a da su bude ido tare da gane kudin jabu a ciki da wajen jihar, jaridar The Nation ta ruwaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel