Gwamna Masari ya gargadi Jam’iyyar APC a game da tabarbarewar zaman lafiya
Mai girma gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya gargadi jagorori da ‘ya ‘yan jam’iyyar APC mai mulki su farka daga gyangyadin da su ke yi, su tashi tsaye tun da wuri.
Rt. Hon. Aminu Bello Masari ya ja-kunnen jam’iyyar APC a jihar Katsina da cewa rashin tsaro da ake fama da shi a gwamnatinsu zai iya yin sanadiyyar rasa mulkinsu a zabe mai zuwa.
Jaridar Katsina Post ta ce Aminu Bello Masari ya yi kira ga ‘ya ‘yan jam’iyyarsa su kara kokari a yakin da ake yi da ‘yan bindiga, ‘yan fashi da makami da masu satar dabbobin Bayin Allah.
Jihar Katsina ta na cikin jihohin da miyagun ‘yan bindiga su ke hallaka mutane a cikin kauyuka.
Gwamna Aminu Masari ya yi wannan kira ne a lokacin da ya ke magana da shugabannin APC da masu ruwa da tsakin jam’iyya na mazabu 361 da kananan hukumomi 34 na jihar Katsina.
Masari ya tunawa jam’iyyarsa ta APC cewa sun kori PDP daga mulki ne saboda gwamnatin wancan lokaci ta gaza shawo kan kalubalen rashin tsaro da ake fama da shi a kasar.
KU KARANTA: Sanata ya sha ban-ban kan batun sauke Shugabannin Sojoji
Gwamnan ya ce za ayi rashin dabara muddin jam’iyyar APC mai mulki a yau ta bari aka yi waje da ita daga kan kujerar gwamnati saboda irin wannan dalili na rashin zaman lafiya
“Sukar gwamnati da cewa ba ta kokari a bangaren tsaro ya na neman zama wani salon yakin neman zaben 2023.” Inji gwamna Masari.
Gwamnan ya yabi gwamnatin tarayya da cewa: “Babu shugaban da ya kashe kudi wajen matsalar rashin tsaro a Najeriya irin Muhammadu Buhari tun da aka dawo mulkin farar hula.”
Gwamnan na APC ya kara da cewa: “Mun gujewa ba masu garkuwa da mutane da ‘yan fyade bayanai game da jama’a da shirin jami’an tsaro da sojoji.”
A cewar gwamnan, sojoji kadai ba za su iya kawo zaman lafiya a jihar Katsina ba. Masari ya ce dole sai kowa ya taka rawar gani, ya bukaci ‘yan APC su ba jami’an tsaro hadin-kai.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng