Buhari ya yi ta'aziyyar Umar Gana, jigo a jam'iyyar APC

Buhari ya yi ta'aziyyar Umar Gana, jigo a jam'iyyar APC

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi martani a kan mutuwar wani babban jigon jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Alhaji Umar Gaba.

Alhaji Umar Gana ya rasu ne a ranar Talata, 21 ga watan Yuli, bayan gajeriyar rashin lafiya.

A wani rubutu da mai magana da yawun shugaban kasar, Mallam Garba Shehu ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya ce Buhari na mika ta'aziyyarsa a kan mutuwar jigon na APC.

KU KARANTA KUMA: Yadda Isma'ila Funtua da wasu suka so sasanta wa da ni a yayin da nake tsare - Sowore

Ya wallafa a shafin nasa: "Shugaban kasa Muhammadu Buhari na mika ta'aziyyar ga iyalai, jam'iyyar All Progressives Congress (APC), gwamnati da daukacin jama'ar jihar Kaduna a kan mutuwar Alhaji Umar Gaba a ranar Talata bayan 'yar rashin lafiya.

Buhari ya yi ta'aziyyar Umar Gana, jigo a jam'iyyar APC
Buhari ya yi ta'aziyyar Umar Gana, jigo a jam'iyyar APC Hoto: The Cable
Asali: UGC

"Shugaban kasa ya tuna da tarin gudumawar da Alhaji Gana ya bada a 2015 da 2019 yayin zaben shugaban kasa da na gwamnoni, inda ya kasance jagora kuma mamban kwamitin yakin neman zaben.

"Shugaba Buhari ya yi addu'an Allah ya bai wa iyalansa hakurin jure rashin jajirtaccen dan siyasar tare da yin Rahama garesa."

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: Mutum 8 sun rasa rayukansu a sabon rikicin Zangon Kataf

A wani labarin, a ranar Litinin, 20 ga watan Yuli, 2020 ne aka samu labari bagatatanwastam cewa Malam Isma’ila Isa Funtua ya rasu bayan ya samu bugun zuciya.

Isma’ila Isa Funtua ya na cikin manyan na-hannun daman shugaban kasa Muhammadu Buhari, kuma surukinsa ne bayan abokantakar da ke tsakaninsu.

Shugaban kasar ya yi jawabi ta bakin Garba Shehu ya na nuna takaicin wannan rashi, inda ya aika sakon ta’aziyya ga ‘yanuwan marigayin da kuma mutanen Katsina.

“Cikin takaici, shugaba Muhammadu Buhari ya samu labarin mutuwar tsohon abokinsa kuma na kusa da shi, Malam Isma’ila Isa Funtua, wanda ya kasance shugaba ne na kungiyar NPAN.”

Jawabin ya kara da cewa: “Shugaban kasar ya na yi wa iyalai da dangi, da gwamnati da kuma mutanen jihar Katsina da abokai da na-kusa da tsohon shugaban na NPAN, musamman abokansa a harkar aikin jarida ta’aziyyar wannan rashi.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel