Yanzu Yanzu: Buhari ya shiga ganawar sirri da Jonathan

Yanzu Yanzu: Buhari ya shiga ganawar sirri da Jonathan

- Shugaba Muhammadu Buhari ya shiga labule da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan

- Sun shiga ganawar ne cikin sirri a fadar Villa da ke Abuja

- Zuwa yanzu dai ba a san ainahin dalilin ganawar tasu ba

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shiga ganawa da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a fadarsa da ke Abuja.

Goodluck Jonathan ya isa fadar shugaban kasar a safiyar yau Talata, 21 ga watan Yuli.

Har a halin yanzu ba a san abinda suke tattaunawa ba saboda taron na sirri ne suka shiga.

Sai dai an tattaro cewa ganawar baya rasa nasaba da karramawar da shugaba Buhari ya yi wa tsohon Shugaban kasar.

Idan za ku tuna, a baya Legit.ng ta rahoto cewa duk da banbancin siyasa da ke tsakani, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da sanya wa filin jirgin kasa na Agbor sunan wanda ya gada, Goodluck Jonathan.

Rotimi Amaechi, ministan sufuri, ya bayyana hakan a ranar Asabar, 18 ga watan Yuli ta wallafar Twitter da hadimin shugaban kasa, Tolu Ogunlesi yayi.

Ministan sufuri ya ce titin jirgin kasa na Itakpe zuwa Warri daga yanzu za a dinga kiran shi da na Goodluck Jonathan.

KU KARANTA KUMA: Gwamna Fintiri ya yi martani a kan zarginsa da kin kiyaye dokoki a filin jirgi

Amaechi ya ce za a kaddamar da babban aikin ta yanar gizo kuma babban abinda za a fifita shine sufurin kayayyaki ballantana yadda titin jirgin ya ratsa ta Ajaokuta.

"Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da kiran filin jirgin kasa na Agbor wanda ya fara daga Itakpe zuwa Warri, da sunan Goodluck Jonathan. Daga yanzu sunan wurin filin jirgin kasa na Goodluck Jonathan," Tolu Ogunlesi yace.

Da aka bukaci sanin lokacin da za a kaddamar, ya ce: "Wannan ya dogara neda lokacin da ma'aikatar ta samu yarjewar shugaban kasa. Muna tunanin kaddamar da shi ta yanar gizo saboda korona."

A gefe guda, mun ji cewa gwamnatin tarayya ta fara gwajin sabbin jiragen kasa da ta sayo daga kasar China, kamar yadda ministan sufuri, Rotimi Amaechi, sanar da yammacin yau, Juma'a.

Da ya ke sanar da hakan a shafinsa na tuwita, Amaechi ya bayyana cewa an fara gwajin sabbin jiragen a kan sabbin titunan jirgin kasa da aka gina daga Itakpe zuwa Warri.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng