Jirgin soji ya yi hatsari, ya kashe sojoji biyu bayan fadawa teku

Jirgin soji ya yi hatsari, ya kashe sojoji biyu bayan fadawa teku

Akalla mutane biyu ne suka mutu a hatsarin jirgin sojojin 'Dutch' wanda ya fada cikin teku jim kadan bayan tashinsa daga tsibirin Caribbean a Aruba, a cewar ma'aikatar tsaro ta Netherlands a ranar Litinin.

Jirgin, mai saukar ungulu, na kan hanyarsa ta zuwa tsibirin Curacao a lokacin da ya rikito kusan kilomita 12 zuwa cikin tekun Aruba, a cewar ma'aikatar.

"Sojoji biyu daga cikin tawagar mutane hudu da ke akan jirgin sun mutu," cewar Rob Bauer, shugaban rundunar sojin Dutch, a taron manema labarai a garin Hague.

"Sauran mambobin jirgin guda biyu sun samu raunuka," a cewarsa, yana mai kiran hatsarin da "rahoto mai muni" da kuma "

Har yanzu ba a san dalilin faduwar jirgin ba, amma dai wani jirgin mai saukar ungulu mallakar rundunar sojin kasar Hollan ya isa wurin domin neman na'urar adana bayanai ta jiragen sama, kamar yadda Bauer ya bayyana.

Kazalika, Bauer ya bayyana cewa neman akwatin zai bawa rundunar soji wahala saboda iska mai karfi da manyan igiyar ruwa da ke kadawa a saman tekun.

KARANTA WANNAN: Akwai sabuwar annobar da ke jiran Nigeria - Gwamnatin tarayya

Jirgin soji ya yi hatsari, ya kashe sojoji biyu bayan fadawa teku
Jirgin soji ya yi hatsari, ya kashe sojoji biyu bayan fadawa teku Source: Twitter
Asali: Twitter

A kasa Nigeria kuwa, Gwamnatin tarayya ta ce Nigeria zata fuskanci wata babbar annoba ma damar ta kasa amfani da yanayin da annobar COVID-19 wajen bunkasa fannin kiwon lafiya.

Sakataren gwamnatin tarayya (SGF) Mr Boss Mustapha ya bayyana hakan a lokacin kaddamar da hukumar kwararru (BoE) na shirin bincike da bunkasa kiwon lafiya (HSRDIS) a Abuja.

DUBA WANNAN: Binciken badakala: Shugaban hukumar NDDC ya tayar da bori, ya fadi 'warwas' a gaban kwamiti

A cewar sa: "Idan har muka tsallake wannan yanayin, to lallai zamu fuskanci wata annobar kuma ba zamu iya tsinana komai ba.

"Idan da ace mun bunkasa fannin kiwon lafiya a lokacin annobar Ebola, da bamu sha wahalar da muka sha a yanzu ba, tunda cibiyoyin gwajin COVID-19 biyu kadai garemu."

Ya kara da cewa: "Idan da zaka zagaya kasar nan, zaka samu sama da cibiyoyin kiwon lafiya 10,000, amma kalilan ne ke da kayan aiki, wasu ma ba a amfani da su."

Ya roki mambobin kwamitin kwararrun da su yi bincike kan gine ginen gwamnati na kiwon lafiya banda bangaren aikin da aka dauke su.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel