Rukaiya El-Rufai ta zama macen farko da ta samu aiki da PwC daga Arewa

Rukaiya El-Rufai ta zama macen farko da ta samu aiki da PwC daga Arewa

Rukaiya El-Rufai ta samu aiki da babban kamfanin na PricewaterhouseCoopers Nigeria, wannan ya sa ta zama macen Arewa ta farko a tarihi da ta fara aiki da kamfanin.

A shekarar bana ne Rukaiya Bashir El-Rufai ta shiga sahun wanda za su yi aiki da wannan kamfani da ake ji da shi a Duniya kamar yadda kamfanin bayyana a makon jiya.

Sauran wadanda za su yi aiki da kamfanin sun hada da Akinyemi Akingbade, Chioma Obaro, Kunle Amida, Olusola Adewole. Sai kuma Tosin Labeodan, Wura Olowofoyeku, da Yinka Yusuf.

Wannan ne karon farko da aka samu mutumiyar Arewacin Najeriya a PricewaterhouseCoopers Nigeria.

Hajiya Rukaiya Bashir El-Rufai mai shekara 37 ta yi karantun ilmin fannin akawu a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, ta kuma fita da matakin digiri na biyu.

A 2007 ne El-Rufai ta samu shaidar Digirgir a bangaren gudanarwa a babbar makarantar tattalin arziki da ilmin siyasa da ke Landan.

KU KARANTA: Farfesa ‘Dan Najeriya ya zama Shugaban Jami’ar Ingila

Rukaiya El-Rufai ta zama macen farko da ta samu aiki da PwC daga Arewa
Rukaiya El-Rufai Hoto: Twitter/Rukky El-Rufai
Asali: Instagram

Bayan shekara guda kuma ta sake samun Digigir a fannin tsare-tsaren gwamnati a wata jami’a a kasar Jamus.

El-Rufai ta yi aiki da wani kamfanin tattalin arziki a kasar Ingila bayan ta kammala jami’a. Kafin nan ta yi aiki a ofishin PwC da ke Abuja da Legas a lokacin ta na ‘yar makaranta.

Wannan Baiwar Allah ta taba aiki a matsayin mai nazarin tattalin arziki a kamfanoni irinsu IHS Nigeria, Etisalat, KPMG Professional Services da kuma Deloitte & Touche.

A 2020 ne ta yi dacen dawowa PricewaterhouseCoopers Nigeria wanda ya na cikin manyan kamfani hudu a Duniya da su ka yi fice wajen binciken kudi.

A shekarun bayan nan Rukaiya Bashir El-Rufai ta yi aiki da ministar kudin Najeriya a matsayin mai bada shawara, ta kuma jagoranci tsare-tsaren da aka kawo a ma’aikatar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel