Yamah Musa: ‘Yan Majalisar Dattawa sun yi kaca-kaca da mai neman zama Jakada
- Wani wanda aka tura sunansa a matsayin sabon Jakada bai ji dadi a hannun Majalisa ba
- Yamah Musa ya samu matsala lokacin da aka tambaye sa game da gudumuwarsa a APC
- Sanatocin sun yi tir da amsar da Musa ya bada yayin da ake kokarin tantancesa a majalisa
Yamah Mohammed Musa, wanda fadar shugaban kasa ta aiko sunansa domin a tantancesa a matsayin jakadan Najeriya a kasar waje ya yi gumi a gaban majalisa.
Alhaji Yamah Mohammed Musa, mutumin jihar Edo a Kudu maso kudancin Najeriya, ya yi yunkurin yi wa Sanatoci bayanin gudumuwar da ya bada wajen kafa jam’iyyar APC.
Yamah Musa ya na cikin sunayen mutum 41 da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada a matsayin sababbin jakadun Najeriya zuwa kasashen ketare.
Shugaban kwamitin harkokin kasar waje a majalisar dattawa, Adamu Muhammad Bulkachuwa, ya tambayi Musa ya fadi abin da ya sa ya kamata majalisa ta yi na’am da shi.
Da jin wannan tambaya sai Yamah Mohammed Musa ya bada amsa, ya na tunkaho cewa ya na cikin wadanda su ka gudanar da zaben fitar da gwanin ‘yan majalisar wakilai.
A cewarsa, su ne su ka shirya zaben da shugaban majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila ya samu nasara a karkashin jam’iyyar APC mai mulki da rinjaye.
KU KARANTA: An aikawa Magatakardar majalisa takardar sammaci
“Ina cikin ‘yan jam’iyya da su ke kan gaba wajen gudanar da zaben fitar da ‘yan takarar duka ‘yan majalisar Kudu maso yamma.” Inji Yamah Musa.
Musa ya kara da fadawa Sanata Adamu Muhammad Bulkachuwa cewa: “Daya daga cikinsu shi ne shugaban majalisar wakilan tarayya, Femi Gbajabiamila.”
Wannan amsa da wanda ake sa ran zai zama jakadan ya bada bai yi wa ‘yan kwamitin tantance jakadun dadi ba, har Sanata Ibikunle Amosun ya maida masa amsa mai kaushi.
Tsohon gwamnan Ogun kuma jigo a jam’iyyar APC a yankin da Musa ya ambata, Ibikunle Amosu ya bayyana gudumuwarsa da tarkacen banza kurum.
“Wannan aiki ba abin da za ka rika tunkaho da shi bane domin a matsayinmu na ‘yan jam’iyya, mun san wadanda su ka yi wannan aiki a bayan fage.” Inji Ibikunle Amosun.
Amosun ya kara da cewa: “Ba irin wannan tunanin mu ke so ka tafi da shi kasar waje ba, idan an tabbatar da kai, tun wuri gara ka kauda irin wannan tunani daga kan ka.”
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng