Dakarunmu sun hallaka wasu Miyagu a Jihar Benuwai – Hedikwatar Soji

Dakarunmu sun hallaka wasu Miyagu a Jihar Benuwai – Hedikwatar Soji

Rundunar sojojin kasan Najeriya da ke aiki a yankin Arewa maso tsakiya sun yi nasarar ganin bayan wasu miyagu a wani hari da su ka kai ta sama da kasa kwanan nan.

Dakarun sojojin Operations SAFE HAVEN da na WHIRL STROKE ne su ka kai wani samame ta kasa, tare da harin jiragen yaki ta sararin samaniya a shiyyar Arewacin kasar.

A sakamakon wannan hari, jami’an tsaron sun yi dacen kashe wasu ‘yan bindiga da su ka fitini al'ummar Chambe, da ke karamar Logo, a jihar Benuwai.

Rundunar WHIRL STROKE sun kashe miyagun ‘yan bindiga biyu bayan sun samu labarin ta’adin wadannan Makiyaya a ranar 12 ga watan Yuli. 2020.

Kamar yadda Hedikwatar gidan soja ta bayyana, jami’an tsaron sun bi ‘yan bindigan zuwa kauyen Arufu da ke iyakar jihar Taraba, inda su ka kashe wasu daga cikinsu.

KU KARANTA: 'Yan iskan gari sun hargitsa taron jam'iyyar APC a Bauchi

Dakarunmu sun hallaka wasu Miyagu a Jihar Benuwai – Hedikwatar Soji
Hedikwatar Soji
Asali: Twitter

Sojojin sun yi ba-ta-kashi da bindigogi, su ka yi kaca-kaca da miyagun, inda wasunsu da-dama su ka tsere, bayan an hallaka biyu daga cikinsu.

Manjo Janar John Enenche ya bayyana cewa jami’an sojojin sun kuma yi dacen karbe makaman wadannan ‘yan bindiga da su ka tsere da su ka gaza jurewa arangamar.

Janar John Enenche shi ne jami’in da ke kula da harkojin yada labarai na hedikwatar tsaon Najeriya, ya fitar da wannan jawabi ne a ranar 16 ga watan Yuli, 2020.

A dalilin wannan kokari da sojojin su ke yi, ana samun zaman lafiya a yankin na Najeriya inda a baya, ‘yan bindiga su ka hana Bayin Allah sakat inji jami’in sojan.

Haka zalika hedikwatar ta bayyana cewa Manoma sun koma gona, yayin da ake cigaba da cafke ‘yan bindiga a sakamakon hadin-kan da mutanen gari su ke ba sojoji.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel