Farfesa Charles Egbu ya zama Shugaban Jami’ar Leeds Trinity

Farfesa Charles Egbu ya zama Shugaban Jami’ar Leeds Trinity

Babban malamin Najeriya, Charles Egbu ya zama sabon shugaban jami’ar Leeds Trinity da ke kasar Birtaniya.

A jawabin da jami’ar kasar wajen ta fitar a shafinta na yanar gizo, ta bayyana cewa Farfesa Charles Egbu zai gaji Margaret House wanda za ta sauka daga kujerar.

Jaridar Premium Times ta ce Farfesa Margaret House ta shafe shekaru bakwai a matsayin shugabar wannan jami’a ta Leeds Trinity.

Farfesa Charles Egbu zai koma birnin Leeds da ke Ingila ne domin ya karbi ragamar makarantar da ya yi karatu, ya kuma koyar a da.

Charles Egbu zai shiga ofis a ranar Lahadi 1 ga watan Nuwamban 2020.

Egbu ya yi magana bayan an zabe shi a matsayin shugaban jami’ar, ya ce:

“Na yi farin cikin samun aiki da jami’ar Leeds Trinity; wanda manufofinta su ke kai dalibai ga samun nasara a rayuwa, kuma su ka dace da irin nawa manufofin. Jami’ar ta na da tsawon tarihin karatu, koyarwa da aiki, ina farin cikin cigaba daga ginin da Farfesa House ta daura.”

KU KARANTA: Buhari ya yi magana game da tsare Shugaban EFCC

Farfesa Charles Egbu ya zama Shugaban Jami’ar Leeds Trinity
Farfesa Charles Egbu Hoto: LTU
Asali: Instagram

Farfesan ya bayyana cewa a shirya ya ke ya zauna da dalibai da ma’aikata da ma tsofaffin daliban wannan makaranta, domin kai jami’ar ga ci.

“Ina murnar komawa birnin Leeds inda na shafe farkon shekarun neman ilmi na."

Kamar yadda jami’ar ta bayyana, Egbu ya yi fiye da shekaru 25 ya na karantarwa a manyan makarantu. Kafin yanzu ya rike jami’ar East London da ke Ingila.

Farfesan ya taba zama shugaban sashen koyar da gine-gine a jami’ar London South Bank, kuma shugaban tsangayar gine-gine a jami’ar Salford.

Bayan haka ya yi aiki da jami’o’i irinsu UCL, Glasgow, Galedonian University da jami’ar Leeds Beckett wanda aka fi sani da Leeds Metropolitan.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel