Majalisar FEC ta bada shawarar batar da N12.66 a shekara mai zuwa

Majalisar FEC ta bada shawarar batar da N12.66 a shekara mai zuwa

A ranar Laraba, majalisar zartarwa ta gwamnatin tarayya, FEC, ta amince da kudirin tsare-tsaren kashe-kashen kudin Najeriya watau MTEF/FSP na shekarar 2021-2023.

Gwamnatin kasar ta yi hasashen tsara kundin kasafin kudin Naira tiriliyan 12.66 a matsayin abin da za a batar a wadannan shekaru uku masu zuwa a jere.

Da ya ke Magana da ‘yan jarida bayan taron FEC na mako-mako, karamin ministan kasafin kudi, Mista Clement Agba ya bayyana wannan.

An yi wannan taro ne a ranar 15 ga watan Yuli, 2020, kamar yadda aka saba a cikin fadar shugaban kasa da ke babban birnin tarayya Abuja.

Clement Agba ya bayyana cewa gwamnati ta yi lissafin kudin gangar man fetur a kan $40, tare da hangen cewa duk rana za a hako ganguna miliyan 1.6 a Najeriya.

Bayan haka gwamnatin tarayya ta tsaida hawan farashin kaya a kan 11.9%, tare da motsawar karfin tattalin arziki watau GDP da 3%, da kuma N7.5 a matsayin kudin shiga.

KU KARANTA: Majalisa ta dura kan masu fyade a Najeriya

Majalisar FEC ta bada shawarar batar da N12.66 a shekara mai zuwa
Clement Agba
Asali: Twitter

Ministan ya bayyana cewa a karshen wannan shekara ta 2020, jimillar kasafin kudin kasar zai tsuke da -4.42%, daga baya kuma ana sa rai zai habaka zuwa -1.8%.

Ko da cewa a wannan shekara, gwamnati ta na hangen kudin shigan N5.84tr, a shekara mai zuwa ana sa ran abin da zai shigo asusun gwamnatin tarayya zai kai N7.5tr.

A cewar ministan, man da Najeriya za ta saida a shekara mai zuwa ba zai kai na bana ba, a dalilin sabon tsarin da kungiyar OPEC ta shigo da shi kwanan nan.

Gwamnati za ta samo ragowar kudin da za a kashe a kasafin na badi ne ta hanyar cin bashi da makamantan hakan. Yanzu haka Najeriya ta na biyan bashin da ta ci a baya.

Ministan ya ce ma’aikatar DMO ce ta ke da alhakin yi wa gwamnati bayani game da yadda za ta rika nemo aron kudi.

A tarihin gwamnatin tarayya, ba a taba yin kasafin kudin da ya kai Naira tiriliyan 12 ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel