‘Yan bindiga sun sace wani jami’in hukumar kula da shige da fice da matarsa, sun kuma kashe kanwarsa a Nasarawa
Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kai farmaki gidan wani jami’in hukumar kula da shige da fice na Najeriya, Salihu Usaman, a garin Gudi da ke karamar hukumar Akwanga na jihar Nasarawa.
Sun kuma yi garkuwa da jami’in da kuma matarsa.
Wani idon shaida, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce yan bindiga sun kai mamaya gidan da misalin karfe 9:00 na daren ranar Talata.
Majiyan ya bayyana cewa ‘yan bindigan sun yi harbe-harbe domin tarwatsa matasa, wadanda suka yi kokarin dakile harin, sannan harbin ya samu mutum guda.
A cewar majiyar, ‘yan bindigan sun samu shiga gidan bayan sun tsoratar da matasan sannan suka sace jami’in da matarsa.
Wani shaida ya ce, wanda aka sacen ya kasance dan uwan tsohon ministan sadarwa, Mista Labaran Maku.
Da aka tuntube shi, Kwanturolan hukumar a shige da fice a jihar, Zainab Lawal, ta tabbatar da lamarin.
KU KARANTA KUMA: Shugaban kungiyar kwadago na Najeriya reshen jihar Taraba ya rasu sakamakon cutar korona
Ta ce: “An sace jami’in NIS, Superintendent Salisu Usman da matarsa.
“An kuma harbi kanwarsa inda hakan ya yi sanadiyar mutuwarta.”
Kakakin yan sandan jihar, ASP Ramhan Nansel, bai amsa kiran waya ba a daidai lokacin kawo wannan rahoto kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
A wani labari makamancin wannan, mun ji cewa 'Yan bindiga sun sace babban limamin rundunar 'yan sandan jihar Taraba, Mallam Mustapha Nuhu.
An yi garkuwa da babban dan sandan ne a daren ranar Lahadi, 12 ga watan Yuli, jaridar Daily trust ta ruwaito.
'Yan bindigar da za su kai 10 sun tsinkayi gidan Malamin da ke kwatas din Nana Aisha a tsakar dare tare da sace shi.
Malamin kuma babban dan sandan, na aiki da rundunar 'yan sandan jihar Taraba.
An gano cewa yayi wa'azi a kan yawaitar laifuka musamman garkuwa da mutane a jihar Taraba yayin hudubar ranar Juma'a.
Jaridar Daily Trust ta gano cewa, 'yan bindiga na ta kai hari a tsakiyar birnin Jalingo a cikin makonnin nan.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng