‘Yan fashi sun sanar da Jama'a da Ma’aikatan banki game da shirin hari a jihar Ebonyi

‘Yan fashi sun sanar da Jama'a da Ma’aikatan banki game da shirin hari a jihar Ebonyi

Wasu ‘yan fashi sun rubuta takarda zuwa ga bankuna cewa za su kawo hari. Wannan lamari ya tada hankalin mazauna garin Afikpo, karamar hukumar Afikpo ta Arewa, jihar Ebonyi.

A ranar Talata, 14 ga watan Yuli, 2020, jaridar Punch ta rahoto cewa ‘yan fashi sun aikawa bankunan da ke cikin yankin Afikpo takarda cewa a saurari zuwansu.

An tanadi jami’an ‘yan sanda, da sojoji da wasu jami’an tsaro da ke jihar domin a ga bayan wadannan ‘yan fashi da su ke shirin shigowa cikin garin Afikpo.

Jaridar ta bayyana cewa yanzu an baza jami’an tsaro da motocin aiki a duk wasu muhimman wurare da ke kan iyakokin shiga da fita daga hakaramar hukumar.

Kantomar karamar hukumar Afikpo ta Arewa, Misis Amuche Otunta ba ta iya tabbatar da gaskiyar lamarin da ake ji na cewa ‘yan fashi sun aiko wasikar kawo hari ba.

Amuche Otunta ta shaidawa ‘yan jarida cewa: “Abin da na sani kurum shi ne akwai barazanar tsaro a karamar hukuma ta.”

KU KARANTA: Mun tuba: Mayakan Boko Haram sun tsira bayan barin kungiyar ta'adda

‘Yan fashi sun sanar da Jama'a da Ma’aikatan banki game da shirin hari a jihar Ebonyi
Kwamishinan 'Yan Sandan jihar Ebonyi
Asali: Facebook

Otunta ta ke cewa: “Kun tuntubi DPO? Su wa ‘yan fashin su ka aikowa wasikar? Ku tambayi DPO, shi ne babban jami’in tsaro na karamar hukumar.”

“Kun ce ‘yan fashi sun aikowa mutanen gari wasika. Ban san mutanen da su ka karbi takardar ba.” Otunta yayin da ta ke amsa tambayoyi.

Kantomar ta kara da cewa: “Amma game da wannan lamari, na san cewa akwai matsalar tsaro, amma ban san ko ‘yan fashi sun rubuta wata wasika ba.”

Kakakin ‘yan sandan jihar Ebonyi, Loveth Odah, ba ta yi magana da ‘yan jarida yayin da aka kira ta a wayar tarho ba.

Amma wani jami’in ‘dan sanda wanda bai bari an bayyana sunansa ba, ya tabbatar da cewa babu shakka ‘yan fashi sun aiko takarda cewa za su kawo hari.

Haka zalika wani Matashi, Eze Egwu ya tabbatar da wannan batu, ya ce an aiko masu wasika.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel