Zamfara da Sokoto: Sojoji sun ceto mutum 5 tare da ragargaza wasu 'yan bindiga

Zamfara da Sokoto: Sojoji sun ceto mutum 5 tare da ragargaza wasu 'yan bindiga

- Rundunar Operation Hadarin Daji yi gagarumin nasara a kan 'yan bindiga a jihohin Sokoto da Zamfara

- Dakarun rundunar sojin sun ceto mutum 5 tare da ragargaza wasu 'yan bindiga

- Sun kuma samu shanu 302 tare da tumakai 412, sun kuma samu wayoyin tafi da gidanka guda biyar

Rundunar Operation Hadarin Daji na ci gaba da kokarin tabbatar da zaman lafiya tare da fatattakar rashin tsaro a yankin arewa maso yamma.

Dakarun na ci gaba da halaka 'yan bindigar da suka addabi yankin.

A ranar 11 ga watan Yuin 2020, bayan samun bayanan sirri a kan 'yan bindigar da kuma kwashe shanu da suka yi a kauyukan Daki Takwas, Tashar Katuru da kuma Talatan Mafara a jihar Zamfara, rundunar ta tura dakarunta yankin.

Zamfara da Sokoto: Sojoji sun ceto mutum 5 tare da ragargaza wasu 'yan bindiga
Zamfara da Sokoto: Sojoji sun ceto mutum 5 tare da ragargaza wasu 'yan bindiga Hoto: Hedkwatar tsaro
Asali: Facebook

Dakarun sun yi nasara a musayar wuta da ta shiga tsakaninsu da 'yan bindigar. Sun kashe wasu daga cikin yan ta'addan yayin da wasu suka tsere da raunika.

Cike da nasara, sun samu shanu 302 tare da tumakai 412, sun kuma samu wayoyin tafi da gidanka guda biyar. Ana ci gaba da kokarin sada dabbobin da masu su.

A wani ci gaba na daban, an ceto mutum 2 da aka yi garkuwa da su a karamar hukumar Isa ta jihar Sokoto.

Hakazalika, dakarun sun ceto wasu mutum 2 a kauyen Yayi da ke karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto.

Bayan tambayarsu da aka yi, an gano cewa an yi garkuwa da su tun ranar 1 ga watan Yunin 2020. An mika su ga gwamnatin jihar Sokoto.

KU KARANTA KUMA: Wata sabuwa: Ana tuhumar Magu a kan gidaje 332 da jiragen ruwa na man fetur 2

Hedkwatar tsaro ta wallafa a shafinta na twitter cewa: "Rundunar Operation Hadarin Daji sun kashe ‘yan bindiga da dama, sun ceto mutanen da aka yi garkuwa da su da kuma kwato dabbobi da aka sace a ihohin Sokoto da Zamfara."

Kakakin rundunar sojin, John Enenche ya sanar, ya ce yayin sintirin rundunar dakarun a ranar 10 ga watan Yulin 2020, sun damko wasu kungiyoyin 'yan sa kai biyar da wani wurin gyara bindiga a kan titin kauyen Maga zuwa Kyabu zuwa Tadurga.

An samu bindigogi 10 na toka, gwafa, suka da babur. An samu zarto daya, fulogi 16, gatari daya da wayoyi 3.

Hukumar sojin na jinjina ga zakakuran dakarun a kan sadaukantakarsu da jajircewarsu. Ta kara kira garesu da su ci gaba da kokarin ganin bayan makiyan kasarmu ta gado.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel