Rashin tsaro: 'Yan bindiga sun barmu da zawarawa 500 da marayu 1,600 - Sarkin Ruman Katsina

Rashin tsaro: 'Yan bindiga sun barmu da zawarawa 500 da marayu 1,600 - Sarkin Ruman Katsina

- Hakimin Batsari kuma Sarkin Ruman Katsina, Alhaji Mohammed Muazu, ya yi bayanin irin ta'asar da hare-haren yan bindiga ya yi masu

- A kwanan nan ne 'yan bindiga suka kai kauyen 'Yar Gamji da ke jihar inda suka kashe manoma 15

- Daga cikin barnar da ayyukan ta'addancin ya yi, ya ce yanzu haka akwai mata zawarawa kusan 500 da yara marayu 1,600

Alhaji Mohammed Muazu ne hakimin Batsari da ka karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina. Shine kuma Sarkin Ruman Katsina.

Ya samu zantawa da jaridar The Punch a kan harin kwanan nan da 'yan bindiga suka kai kauyen 'Yar Gamji inda suka kashe manoma 15.

Basaraken ya yi bayanin yadda wannan harin ya matsantawa rayuwar mazauna yankin.

Kamar yadda Sarkin Ruman Katsina ya sanar bayan tambayarsa da aka yi yadda ya ji a kan harin da ya halaka manoma, ya ce wannan mummunan al'amari ne.

"A kowacce rana, 'yan bindiga na kai mana hari. Wannan harin da aka kai 'Yar Gamji ba a cikin gari aka yi ba, a gonaki aka kai harin.

"Wurin karfe 11 na safe aka kai harin yayin da ma'aikatan ke gonakinsu. Sun kashe mutum 15 yayin da suka raunata mutum 2 kafin zuwan jami'an tsaro.

"Sabon harin ya haddasa tsoro a zukatan jama'a," cewar hakimin.

Rashin tsaro: 'Yan bindiga sun barmu da zawarawa 500 da marayu 1,600 - Sarkin Ruman Katsina
Rashin tsaro: 'Yan bindiga sun barmu da zawarawa 500 da marayu 1,600 - Sarkin Ruman Katsina Hoto: The Nation
Asali: UGC

Ya kara da cewa, "a halin yanzu jama'a basu zuwa gonaki saboda tsoro. A garuruwa da kayuka masu tarin yawa, mutane na bacci ne da ido daya.

"Mun san gwamnati na kokari amma muna kira gareta da ta kawo dauki karamar hukumar Batsari.

"Noma ana yin shi ne a Ruma, Batsari, Wagini da Abadau kadai kuma muna da kauyuka 200."

Ya koka da yadda suka yi muguwar asara don yace ba zai iya bayyana asarar nawa suka yi ta kudi ba.

KU KARANTA KUMA: Yadda Buhari ya bai wa DSS umarnin bincikar Magu tun 2018

Ya ce, "Mun rasa rayukan mutum 300. Mata zawarawa akwai kusan 500 da yara marayu 1,600.

"A halin yanzu makarantun da 'yan gudun hijira ke zama duk sun cika. Sun kwashe mana dabbobi kusan miliyan uku zuwa hudu. Bamu da kwanciyar hankali.".

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel