An kama wasu mutum 12 da ake zargi da fataucin miyagun kwayoyi a jihar Niger

An kama wasu mutum 12 da ake zargi da fataucin miyagun kwayoyi a jihar Niger

- Humumar NDLEA reshen ihar Niger Niger ta kama wasu mutum 12 da ake zargin masu fataucin miyagun kwayoyi ne, ciki harda hodar iblis

- An yi kamen ne a lokacin kullen COVID-19 a jihar wanda ya yi sanadiyar hauhawan lamarin fataucin miyagun kwayoyi

- Mukaddashin kwamandan NDLEA, Isaac Aloye ya tabbatar da lamarin, ya ce wadanda ake zargin sun nannade kayayyakin a tsanaki cikin dabaru daban-daban

- A halin yanzu an tura shida daga cikin wadanda ake zargin kotu, sauran shida na nan ana bincikensu har yanzu domin samun karin bayanai

Hukumar kula da hana fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya (NDLEA) a jihar Niger ta kama wasu mutum 12 da ake zargin masu fataucin miyagun kwayoyi ne, ciki harda hodar iblis.

Channels TV ta ruwaito cewa an yi kamun ne a lokacin kullen COVID-19 a jihar wanda ya yi sanadiyar hauhawan lamarin fataucin miyagun kwayoyi.

Da yake tabbatar da lamarin, mukaddashin kwamandan NDLEA, Isaac Aloye, ya ce wadanda ake zargin sun nannade kayayyakin a tsanaki cikin dabaru daban-daban.

Ya kara da cewar an tura kayayyakin a matsayin sakonni daga wurare daban-daban na kasar, ta motoci masu dauke da lasisin tafiya na COVID-19 domin samun damar wucewa.

KU KARANTA KUMA: Magu yana sayarwa abokansa wasu kadarorin gwamnati da ya ke ƙwato wa - Fayose

An kama wasu mutum 12 da ake zargi da fataucin miyagun kwayoyi a jihar Niger
An kama wasu mutum 12 da ake zargi da fataucin miyagun kwayoyi a jihar Niger Hoto: Channels TV
Asali: UGC

Aloye ya bayyana cewa da kayan sun samu wucewa garuruwan da aka yi niyan turasu a jihar idan ba don jami’ansa masu sanya idanu ba wadanda suka kama su a wurare mabanbanta.

Kayayyakin sun hada da tabar wiwi mai nauyin sama da kilo dubu daya, Arizona mai nauyin kilo 30 da kuma hodar iblis.

KU KARANTA KUMA: Fasinjoji sun lakaɗawa direba duka ya mutu saboda tukunkumin fuska

Daya daga cikin wadanda ake zargin mai shekaru 41, Enuma Uchenna, ya yi ikirarin cewa wani abokinsa ne ya bukaci ya taya shi daukar tukunyar gas dinsa ciki harda hodar iblis daga wani garejin mota, cewa bai da masaniyar abun da ke ciki.

Yayinda aka tura shida daga cikin wadanda ake zargin kotu, sauran shida na nan ana bincikensu har yanzu domin samun karin bayanai.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel