Ba ni da gidan N800m, ni ma haya na ke yi – Kiki Osinbajo ta karyata jita-jita

Ba ni da gidan N800m, ni ma haya na ke yi – Kiki Osinbajo ta karyata jita-jita

‘Diyar mataimakin shugaban kasar Najeriya, Kiki Osinbajo, ta karyata jita-jitar da ake yi na cewa ta na da wani gida da darajarsa ta kai Naira miliyan 800 a Abuja.

Ana jita-jitar cewa Kiki Osinbajo mai shekara 27 a Duniya ta na da gida a yankin Highbrow da ke cikin unguwar Wuse 2 a babban birnin tarayya Abuja.

Kiki ta fito ta ce babu gaskiya a wannan labari. ‘Diyar mataimakin shugaban kasar ta musanya wannan ne a shafinta na Instagram a yau Juma’a, 10 ga watan Yuli.

A cewar wannan Baiwar Allah, gidan da ake maganar cewa na ta ne, haya ta ke yi a cikinsa.

“Ga ni, abin mamaki ne yadda babban mutum zai zauna a cikin gidansa ya yi karya a game da ni; babban mutum wanda watakila ya na da ‘ya ‘ya sa’anni na!”

Osinbajo ta kara da cewa: “Kamar sauran ‘yanmata a Najeriya, ina neman na kai na.”

KU KARANTA: Sarki Bayero ya tashi tsaye a kan lalata da ake yi da kananan yara

Ba ni da gidan N800m, ni ma haya na ke yi – Kiki Osinbajo ta karyata jita-jita
Jackson Ude da Kiki Osinbajo
Asali: Instagram

Misis Kiki Osinbajo ta na cikin shahararrun ‘yan kasuwa masu tasowa a Najeriya, har ta ta taba samun wata kyauta saboda irin kokarinta.

Ta ce: “Watakila abin ya ba mutane irin sa mamaki cewa ‘yan mata za su iya zagewa su nemi na kansu. Kowa ya na iya bincike ya gano wanda ya mallaki gidan Glamd Africa da ke Abuja.”

“Ni ‘yar haya ce a gidan. Sunan uban gida na Musa Adams.” inji ta.

Jackson Ude wanda ya yi aiki da gwamnatin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan shi ne ya fara kawo labarin cewa Kiki Osinbajo ta mallaki wannan gida na Naira miliyan 800.

Mai gidan jaridar na Point Blank News bai tsaya nan ba, yanzu haka mataimakin shugaban kasa ya bada umarnin ayi bincike a kansa bayan ya zarge shi da karbar kudi daga hannun Ibrahim Magu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng