Jakadan kasar Lebanon ya fice daga ofishin Majalisar Tarayya yayin taro

Jakadan kasar Lebanon ya fice daga ofishin Majalisar Tarayya yayin taro

- Majalisar Wakilan Tarayya ta gayyaci Jakadan Lebanon domin ya amsa wasu tambayoyi

- Houssam Diab ya tashi ya yi tafiyarsa yayin da ‘Yan Majalisa su ka shirya ganawa da shi

- Shugabar kwamitin harkokin kasar waje a Majalisar kasar ta fusata da wannan wulakanci

A ranar Alhamis, 8 ga watan Yuli, 2020, Jakadan Lebanon a Najeriya, Houssam Diab, ya fice daga zauren majalisa yayin da kwamitin harkokin kasar waje ke shirin zama da shi.

An gayyaci Houssam Diab a majalisar ne domin ya amsa wasu tambayoyi a game da cin kashi da wulakancin da ake zargin ana yi wa mutanen Najeriya a kasar sa ta Lebanon.

Ana zargin cewa mutanen kasar Lebanon su na muzgunawa ‘yan Najeriya da ke kasar wajen, inda a cikin ‘yan kwanakin labarin wata Temitope Arowolo ya zagaye Duniya.

A daidai lokacin da ake shirin fara wannan ganawa, Jakadan kasar ta Lebanon ya tashi ya yi tafiyarsa. Rahotanni sun ce hakan ya faru ne da kimanin karfe 11:00 na safe.

Wannan abu da wakilin kasar da ta ke zaman mutunci da Najeriya ya yi, bai yi wa ‘yan majalisar wakilai dadi ba bayan sun sa ran jin ta bakin wakilin kasar Yammacin Ashiyar.

KU KARANTA: An haramtawa 'Yan Najeriya neman aiki a Dubai bayan an kama Hushpuppi

Jakadan kasar Lebanon ya fice daga ofishin Majalisar Tarayya yayin taro
Hon Akande-Sadipe da Diab Hoto: Lekan Olusada/Twitter
Asali: Twitter

An rahoto shugabar kwamitin harkokin kasar waje a majalisa, Tolulope Akande-Sadipe ta na cewa: “Na yi mamaki da na ga Jakadan ya mike ya yi tafiyarsa, ya bar mu a wurin.”

Honarabul Tolulope Akande-Sadipe mai wakiltar mazabar Oluyole a jihar Oyo ta sallami ‘yan jarida daga dakin taron bayan Jakadan ya yi tafiyarsa.

Akande-Sadipe cikin fushi ta bada umarnin a kira babban taron shugabannin kwamitin bayan yunkurin ganawarsu da Jakadan a gaban kwamiti ya ci tura.

‘Yar majalisar ta ce babu dokar da ta ce sai Jakadan ya halarci taron, illa iyaka dama an shirya zaman ne domin a kara dankon zumuncin da ke tsakanin kasashen biyu.

“Mu na da ‘Yan Najeriya da dama a Lebanon, kuma akwai ‘Yan Lebanon rututu a Najeriya. Tun shekarun 1950s mu ke da alaka da kasar Lebanon.” inji Akande-Sadipe.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel