Yadda Magu ya ci zarafin Abdulsalami da TY Danjuma - Olusegun Adeniyi
Olusegun Adeniyi, shugaban kwamitin tace labarai na Thisday, ya bayyana yadda Ibrahim Magu, dakataccen shugaban hukumar yaki da rashawa da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ya ci zarafin makusantan shugaban kasa Muhammadu Buhari biyu ba tare da sanin shugaban kasar ba.
Adeniyi ya ce, Magu ya toshe wani yunkuri na tsohon ministan tsaro, Theophilus Danjuma, na siyan jirgin sama makonni kadan bayan sun kai samame gidan Abdulsalami Abubakar.
A wata takarda da ya fitar a ranar Alhamis, tsohon mai magana da yawun marigayi shugaban kasa Umaru Musa Yar'Adua, ya ce shugaban kasar ya san abinda Magu ya aikata ne bayan aiwatarwan.
Ana bincikar Magu a gaban wani kwamitin fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan zargin rashawa.
Abubakar Malami, ministan shari'a kuma Antoni Janar na tarayya ya zarge sa da waskar da wasu kudade da aka samo.
Adeniyi ya zargi Magu da yin abinda bai dace ba a kan Danjuma da Abubakar.
Yace koda abinda ya yi daidai ne, bai dace ya aikata hakan ba ba tare da sanin shugaban kasa Muhammadu Buhari ba.
Ya ce: "Tsohon ministan tsaro, Laftanal Janar Theophilus Danjuma mai ritaya, ya je ganin shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadarsa. Hamshakin dan kasuwar man fetur din ya biya kudi don siyan jirgin sama amma an dawo mishi dasu.
"Kamar yadda ma'aikacin bankin ya sanar, Magu ne ya bada umarnin rike kudi.
"Daga abinda na tattara, shugaban kasar ya dauki dogon lokaci kafin ya gamsar da Danjuma cewa bai san abinda Magu yayi ba.
"Makonni kadan kafin nan, jami'an EFCC sun kai samame gidan Abdulsalami Abubakar na Minna inda suka birkitashi. A wannan karon ma shugaban kasar bashi da masaniya.
"Duk da Danjuma da Abdulsalami basu fi karfin shari'a ba, bai kamata a yi amfani da iko don cin zarafin su ba."
KU KARANTA KUMA: Wata sabuwa: Kusoshin EFCC za su amsa tambayoyi a kan binciken Magu
Ya ce an yi korafi ba sau daya ba ga Buhari a kan yadda shugaban EFCC ke yin gwanjon kayan da ya kwace.
"Mutumin da zai taba har da manya da jiga-jigai a kasar nan wadanda suka hada da 'yan uwan shugaban kasa, dole ne a dinga zargin sa," ya kara da cewa.
"A shekaru biyar da suka gabata, Magu ya sha yin ikirari akan daruriwan biliyoyin da aka samo daga mahandama. Amma kuma gwanjon kadarorin ba a yinsu yadda ya dace, hakan yasa ba a bin tsarin da ya dace.
"Tunda Abuja babban birni ne inda mazauna suka san kazamin sirrin junansu, an ta aike wa shugaban kasar korafin cewa Magu ba zai fi karfin hukuncinsa ba."
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng