Hotunan zanga-zanga da aka yi a Abuja, ana so a taso keyar Tinubu a gaba

Hotunan zanga-zanga da aka yi a Abuja, ana so a taso keyar Tinubu a gaba

- An gudanar da zanga-zanga a kan jigon APC Bola Tinubu a jiya a Abuja

- Ana so a yi bincike kan motocin kudin da aka gani a gidan Tinubu a 2019

- Tun ba yau ba ake kiran Ibrahim Magu ya binciki dukiyar ‘dan siyasar

A Ranar Laraba, 8 ga watan Yuli, 2020, wasu mutane sun hau kan tituna a babban birnin tarayya Abuja su na zanga-zanga a kan Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Masu zanga-zangar su na kira ga gwamnati ta kama babban jagoran jam’iyyar APC a Kudu maso yammacin Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

An taso fitaccen ‘dan siyasar a gaba ne a dalilin wasu manyan motocin daukar kudi har biyu da aka gani sun shiga gidansa da rana tsaka a shekarar da ta wuce.

Wannan abu ya faru ne a lokacin da ake shirin gudanar da zaben shugaban kasa a Najeriya. A zaben na 2019, shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya sake samun nasara.

Tsohon gwamnan na Legas bai karyata wannan lamari ba a lokacin da ya yi magana da ‘yan jarida a cikin watan Fubrairun 2019.

KU KARANTA: Osinbajo ya yi magana game da jita-jitar Magu ya ba shi wasu kudi

Hotunan zanga-zanga da aka yi a Abuja, ana so a taso keyar Tinubu a gaba
Zanga-zangar Bola Tinubu Hoto: The Cable
Asali: Twitter

Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa motocin nan su na dauke da kudinsa ne ba kudin da aka dauko daga asusun gwamnati ba.

Jaridar The Cable ta kawo wasu daga cikin hotunana wannan zanga-zanga da aka shirya jiya da rana.

Kawo yanzu da mu ke fitar da wannan rahoto, ‘dan siyasar bai maida martani ga masu kira ga hukumomi da gwamnati su bincike sa ba.

A baya an taba kai korafi gaban hukumar EFCC domin ta binciki zargin da ke kan wuyan Bola Tinubu, amma har yanzu ba kai ga yin komai ba.

Ganin cewa an dakatar da Ibrahim Magu, babu mamaki shiyasa wadannan masu zanga-zanga su ka sake tado batun a kasar.

Hotunan zanga-zanga da aka yi a Abuja, ana so a taso keyar Tinubu a gaba
Zanga-zangar Bola Tinubu Hoto: The Cable
Asali: Twitter

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel