Umar Yusuf: Matashi a Borno ya kera kekunan da za su tallafawa jama’a

Umar Yusuf: Matashi a Borno ya kera kekunan da za su tallafawa jama’a

- Umar Yusuf, wani Matashi daga jihar Borno ya na abin a gani - a yaba

- Yusuf ya na kera kekuna masu kyau duk da cewa bai da isassun kayan aiki

- Idan da Gwamnati za ta taimakawa wannan Bawan Allah, da ya yi fice

Wani Matashi mai suna Umar Yusuf ya nunawa Duniya cewa akwai masu basira a Arewacin Najeriya, inda ya hada wasu kekuna masu ban-kwaye.

Mutane sun fara kira ga gwamnati da hukumomin da ke da alhakin taimakawa wannan matashi wajen cin ma burinsa.

Idan gwamnati ta tallafawa Umar Yusuf, hakan zai zaburar da ire-irensa wajen bayyanawa Duniya basirarsu.

Duk da cewa Yusuf bai da wasu kayan aiki, ya na amfani da hannuwansa wajen kera wadannan kekune wadanda idan aka samu irinsu da yawa za su taimakawa kasar.

Daga cikin hanyar da wadannan kekuna na gida za su taimakawa Najeriya akwai samar da ayyukan yi, da kuma rage kashe kudi wajen shigo da kaya daga ketare.

KU KARANTA: Attijrai 10 da ba su da sa’o’i a cikin masu dukiya a 2020

Umar Yusuf: Matashi a Borno ya kera kekunan da za su tallafawa jama’a
Umar Yusuf Hoto: North East Reporters
Asali: UGC

Wannan matashi mai basira ya na zaune ne a garin Maiduguri, babban jihar Borno a yankin Arewa maso gabashin Najeriya. Ba kasafai aka saba jin labarin masu baiwa irinsa ba.

Kamar yadda mu ka samu labari daga jaridar North East Reporters, Umar Yusuf ya hada irin wadannan kekuna rututu a Maidguri, kuma a shirya ya ke da ya kara hada wasu.

Shagon da matashin ya ke aiki ya na kan titin Gomborun-Ngala a kusa da wani asibitin ‘yan sanda da ke Maiduguri.

Wani Kabir Ajibola ya fito ya na rokon gwamnan Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya taimakawa Yusuf da tallafi yadda zai bunkasa.

Shi ma Abdulhamid Abubakar Girei ya yi irin wannan kira, ya ce a hada Matashin da manyan gwamnatin jihar Borno domin su ga irin rawar da ‘dan kasar su ya ke takawa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel