Tukwicin N5000 aka bani da na kashe mutane bakwai – Dan fashi

Tukwicin N5000 aka bani da na kashe mutane bakwai – Dan fashi

Rundunar yan sanda ta kama wani da ake zargin dan fashi ne mai shekara 30 mai suna Abubakar Namalika, wanda ya tona cewa yana daga cikin wadanda suka kashe wani likita.

Likitan da suka kashe mai suna Okpara Enoch, ya kasance ma'aikaci a cibiyar kiwon lafiya ta tarraya da ke Gusau, jihar Zamfara.

Ya ce ya samu tukwicin N5,000 kan kashe mutane bakwai da ya yi ciki harda marigayi Dr. Opara, jaridar The Nation ta ruwaito.

Mai laifin ya bayyana hakan ne yayinda yake amsa tambayoyi daga manema labarai jim kadan bayan kwamishinan yan sandan jihar Zamfara ya gurfanar da shi a hedkwatar rundunar da ke Gusau a ranar Litinin.

Tukwicin N5000 aka bani da na kashe mutane bakwai – Dan fashi
Tukwicin N5000 aka bani da na kashe mutane bakwai – Dan fashi Hoto: The Nation
Asali: UGC

A cewarsa, wani Shehu Bagewaye, shugaban kungiyarsu yana aiken su sato bayin Allah amma sai ya basu kaso kadan bayan ya karbi kudin fansa.

“Tunda na shiga kungiyar yan bindiga a karkashin jagorancin Shehu Bagewaye, na yi amfani da bindigata ta Ak47 na kashe mutane bakwai a kauyukan Dogon Kade da Gidan Badda da muka kai hare-hare mabanbanta,” in ji Namalika.

Ya kuma tabbatar wa da manema labarai cewa yana daga cikin mutane biyar da suka kai wa marigayi Dr. Okpara Enoch hari a gidansa tare da harbe shi, da cinna masa wuta bayan ya ki basu kudi.

“Ina cikin wadanda shugabanmu, Alhaji Shehu Bagewaye ya tura domin su sato marigayi Dr. Okpara a gidansa da ke yankin Maren a nan Gusau.

"Da muka bukaci ya bamu kudi sai ya fada mana cewa baida shi, sai muka kashe shi sannan muka kona gawarsa muka kuma bar gidan a nan take.” In ji Namalika.

KU KARANTA KUMA: Ibrahim Magu: Dino Melaye ya yi martani a kan dakatar da shugaban EFCC da Buhari ya yi

Don haka, kwamishinan yan sandan, Usman Nagoggo ya bayyana cewa mai lafin ya fallasa laifinsa kuma ya ba yan sanda damar samun bayanai game da mafakar ‘ yan kungiyar.

Ya kuma bayyana cewa za a kai shi kotu bayan bincike.

“Shehu Bagewaye na cikin tubabbun yan bindiga a lokacin da aka yi sulhu harma ya mika komanin bindigogi biyar ga rundunar yan sandan,” in ji kwamishinan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel