Magu: Babu wanda ya fi karfin bincike – Fadar shugaban kasa

Magu: Babu wanda ya fi karfin bincike – Fadar shugaban kasa

- Fadar shugaban kasa ta tabbatar da cewar babu wani mahaluki da ya fi karfin bincike a karkashin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari

- Hakan martani ne ga binciken da ke gudana a kan mukaddashin shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC), Ibrahim Magu

- Ta ce an yi hakan ne domin bashi damar amsa zarge-zargen da ake yi a kansa

Binciken da ke gudana a kan mukaddashin shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC), Ibrahim Magu, ya kasance ne domin bashi damar amsa zarge-zargen da ake yi a kansa.

Akwai alamu da ke nuna cewa babu mamaki dakatarwar da aka yi wa Magu a ranar Talata ya kasance ne sakamakon shawarar da kwamitin da ke bincikensa ya bayar.

Koda dai babu wata majiya na hukuma da ta tabbatar da hakan a daidai lokacin kawo wannan rahoton.

Wata majiya abun dogaro daga fadar shugaban kasa, ta yi bayani kan dalilin binciken Magu.

Ta kuma ce dole ce ta sa kafa kwamitin bincike karkashin jagorancin Ayo Salami saboda tangardar da aka samu wajen yaki da rashawar.

Magu: Babu wanda ya fi karfin bincike – Fadar shugaban kasa
Magu: Babu wanda ya fi karfin bincike – Fadar shugaban kasa Hoto: The Nation
Asali: UGC

Majiyar ta kuma bayyana cewa binciken Magu da ake yi ya nuna cewa babu wani ma’aikacin gwamnati da ya fi karfin a bincike shi duk matsayinsa.

Musamman a yanzu da yake akwai manyan zarge-zarge da ake yi a kan shugaban hukumar yaki da rashawar.

A cewar majiyar: “kwamitin da ke binciken zarge-zargen da ake yi a kan mukaddashin shugaban na EFCC ya kwashe tsawon wasu makonni yana zama.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya nada alkalai 11 na babbar kotun Abuja

“A yarjejeniyar da ke tattarin da tsarin gaskiya da adalci, akwai bukatar ba mukaddashin shugaban hukumar damar amsa tuhume-tuhume da ake masa, wadanda suka kasance masu girman gaske.

“A karkshin gwamnatin Muhammadu Buhari, babu wanda ya fi karfin bincike. Na maimaita: babu wani."

Idan za ku tuna, mun kawo muku rahoton cewa mukaddashin shugaban hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC, na tsare a ofishin yan sanda kuma a nan ya kwana.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel