Zaben Edo: Gwamna Wike ya fi karfin ka – PDP ga Gwamna Ganduje

Zaben Edo: Gwamna Wike ya fi karfin ka – PDP ga Gwamna Ganduje

- PDP ta maidawa Abdullahi Ganduje martani a game da wasu kalamai da ya yi

- Jam’iyyar ta ce Ganduje bai da damar fitowa ya na maganar satar kudin gwamnati

- Kakakin jam’iyyar adawar ya ce Gwamna Wike ba sa’an gwamnan na Kano ba ne

PDP ta bayyana gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje a matsayin ‘sanannen barawo wanda bai da hurumin da zai fito ya yi magana a kan satar dukiyar gwamnati.”

A ranar Litinin, 6 ga watan Yuli, jam’iyyar PDP ta fito ta maidawa Abdullahi Umar Ganduje martani a game da kalaman da ake cewa ya yi game da zaben jihar Edo.

Mai girma Abdullahi Ganduje shi ne shugaban kwamitin da APC ta kafa domin yakin neman zaben gwamna a jihar Edo.

Abdullahi Ganduje ya fito ya na cewa APC za ta turke abokin gabanta, gwamna Nyesom Wike wanda zai jagoranci jam’iyyar PDP wajen samun nasara a Edo.

A wani jawabi da PDP ta yi ta bakin kakakinta, Kola Ologbondiyan, ta ce gwamna Ganduje ya zama tambarin abin kunya tun da aka gan shi ya na sunkuma dala a aljihu.

Jaridar Vanguard ta rahoto PDP ta na cewa: “Abin mamaki, ,mutumin da ake yi wa lakabi da ‘Gandollar’ bayan an kama shi ya na karbar kudi, zai zo ya na zargin wasu da yunkurin sace kudin asusun jiha.”

“PDP ta na nunawa jama’a cewa a jam’iyya irin APC, a mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari ne mutum (irin Ganduje) da bai da mutunci a idon jama’a zai zo fili ya na magana, har ma ya jagoranci yakin neman zabe.”

KU KARANTA: Kafin Wike ya fito daga turkewar da za mu yi masa mun ci Edo - Ganduje

Zaben Edo: Gwamna Wike ya fi karfin ka – PDP ga Gwamna Ganduje
Kakakin PDP Kola Ologbondiyan
Asali: UGC

“Alamu sun nuna cewa gwamna Ganduje da sauran shugabannin APC sun saba da satar dukiyar baitul-mali, ganin inda su ka fara karkata bayan an kaddamar da kwamitin yakin zabe.”

Ologbondiyan ya kara da cewa: “Gwamna Ganduje ya tabbatar da abin da APC ta ke niyya, wanda shi ne ta yi amfani da ‘dan takararta wanda ya ki karbuwa, Osagie Ize-Iyamu, ta yi ram da asusun Edo.”

“…Bayan gwamna Godwin Obaseki ya hana manyan APC wawurar dukiyar gwamnati.” Inji Kola Ologbondiyan

“Jam’iyyarmu ta na fadawa Ganduje cewa ya sani babu Dalar banzar da shi da APC za su sace a jihar Edo. A karkashin mulkin PDP a Edo da sauran jihohi, talakawa ke da mulki ba wasu jiga-jigai ba.”

“Wannan ya sa mutanen Edo su ke tare da Obaseki, su ka yi watsi da APC.”

“A karshe, Gwamna Ganduje da shararren bidiyonsa na “gandollar” ba kanwar lasar Nyesom Wike ba ne.”

PDP ta ce gwamna Wike mutum ne da ake ganin darajarsa, mai gaskiya, amaana da son jama’a, akasin Ganduje.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng